19
Dec
A duk lokacin da aka shiga hunturu, wato lokacin sanyi da iska, wani lokaci ne da yanayi kan canja, wanda kowa da irin yadda yanayin yake zuwa masa, ta yadda wasu sukan samu kansu cikin wani yanayi na ƙunci, wasu kuma a wannan lokaci ne suka fi samun jin daɗin yanayi ta rayuwarsu gaba ɗayanta. Lokacin hunturu, lokaci ne na tsananin sanyi, iska da kuma ƙura, kuma wannan yanki namu na Arewa ne abin ya fi tsanani, ta yadda wasu lokuta ma hatta yanayin samaniya kan canja, a kan yi hadarin sanyi kamar yadda ake yin hadarin ruwan sama. Lokacin…
