29
Apr
Ƙirƙirar 'yan sandan jihohi dai ta kasance batun da ya daɗe ana muhawara a kai a Nijeriya. A ranar Litinin ne Majalisar Wakilan Nijeriya ta gudanar da taron jin ra’ayin jama’a kan maganar samar da ’yan sandan jihohi a faɗin ƙasar. An jima ana tafka muhawara kan batun samar da ’yan sandan jihohi a Nijeriya, sai dai a wannan karon majalisar ta fito ƙarara domin sanya zancen a bainar jama’a. Masu ruwa da tsaki da dama ne suka halarci taron a ranaf Litinin, ciki har da wasu tsofaffin shugabannin qasar da shugabannin addinai da sarakunan gargajiya da sauran su. Amma…
