Siyasa

Kogi, Imo, Bayelsa: Gobe za a gwada ‘imanin’ gwamnatin Tinubu

Kogi, Imo, Bayelsa: Gobe za a gwada ‘imanin’ gwamnatin Tinubu

•Zaɓen farko tun bayan kafuwar gwamnatinsa Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Kimanin masu kaɗa ƙuri’a miliyan 5.2 ne za su fito a ranar 11 ga Nuwamba, 2023 don zaɓen gwamnoni a jihohin Bayelsa, Imo da Kogi. Adedayo Akinwale, ya yi nazari kan matakin shirye-shiryen alƙalan zaɓe, Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa. Yayin da zaɓen gwamnan jihar Bayelsa da Kogi da kuma Imo ke ƙara ƙaratowa a ranar 11 ga watan Nuwamba, jimillar mutane 5,409,438 da suka yi rajista a jihohin uku ke shirin zaɓar sabbin shugabannin zartarwa na jihohin uku. Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa…
Read More
Zaɓen Bayelsa, Imo, Kogi: Ban da nuna halin a-yi-rai-ko-a-mutu, kiran Kwamitin Abdulsalami ga ‘yan siyasa

Zaɓen Bayelsa, Imo, Kogi: Ban da nuna halin a-yi-rai-ko-a-mutu, kiran Kwamitin Abdulsalami ga ‘yan siyasa

Daga BASHIR ISAH Shugaban Kwamitin Wanzar da Zaman Lafiya na Ƙasa, Janar Abubakar Abdulsalami (rtd), ya yi kira ga jam'yyun siyasa da magoya bayansu da a guji nuna halin a-yi-rai-ko-a-mutu yayin zaɓen gwamnonin da za a gudanar ranar Asabar a jihohin Bayelsa da Kogi da kuma Imo. Abdulsalami ya yi wannan kira ne yayin da jam'iyyin siyasa su 18 da za su fafata a zaɓen gwamna a Jihar Kogi suka rattaɓa hannun kan yarjejeniyar zaman lafiya ranar Laraba a jihar. Da yake jawabi ta bakin wakilinsa Cardinal John Onaiyekan, tsohon shugaban ƙasar ya ce: “Wannan taro na da muhimmanci saboda…
Read More
Zaɓuɓɓukan 11 ga Nuwamba: Za mu yi watsi da ƙuri’un duk rumfar zaɓen da aka samu hayaniya – INEC

Zaɓuɓɓukan 11 ga Nuwamba: Za mu yi watsi da ƙuri’un duk rumfar zaɓen da aka samu hayaniya – INEC

Daga BASHIR ISAH Yayin da rage 'yan kwanaki ƙalilan kafin zaɓen gwamna a wasu jihohin Nijeriya, Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta yi gargaɗin ba za ta kula ƙuri'un duk wata rumfar zaɓe da aka fuskanci tashin-tashina ba. Shugaban INEC, Mahmood Yakubu ne ya yi wannan gargaɗi yayin taron masu ruwa da tsaki da ya gudanar ranar Talata a Yenagoa, babban jihar Bayelsa. Ya zuwa ranar 11 ga Nuwamban da ake ciki ne ake sa ran INEC za ta gudanar da zaɓen gwamnoni a jihohin Bayelsa, Kogi da kuma Imo. Yakubu, wanda ya samu wakilcin Kwamishinan INEC mai lura yankunan…
Read More
Manyan jam’iyyu sun bayyana matsayarsu kan shawarwarin Atiku

Manyan jam’iyyu sun bayyana matsayarsu kan shawarwarin Atiku

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Manyan jam'iyyun Nijeriya sun bayyana mabambantan ra'ayoyinsu game da shawarwarin da tsohon ɗan takarar shugaban Nijeriya ƙarƙashin Jam'iyyar PDP Atiku Abubuakar ya bayar. Atiku Abubakar ya bayar da shawara kan tursasawa hukumar zaben Nijeriya INEC amfani da naurar zaɓe da kuma daura sakamako a Internet kafin sanar da wanda ya samu nasara. Ya ce kamata ya yi a riƙa yanke hukuncin shari'un zaɓe gabanin rantsar da wanda aka ayyana ya ci zave idan akwai ƙalubalantar da yake fuskanta ta shari'a. A ganinsa kamata ya yi a mayar da mulkin shugaban ƙasar zango ɗaya na…
Read More
Jam’iyyar PDP ta yi babban rashi

Jam’iyyar PDP ta yi babban rashi

Daga BASHIR ISAH Shugabar Mata ta Jam'iyyar PDP ta ƙasa, Farfesa Stella Effah-Attoe, ta rasu. A cewar ahalin marigayiya, ta rasu ne a ranar Lahadi bayan fama da rashin lafiya. Cikin sanarwar da ta fitar ta bakin sakataren hulɗa da jama'a na ƙasa, Debo Ologunagba a ranar Lahadi, PDP ta bayyana rasuwar Effah-Attoe a matsayin babban rashi ga ƙasa baki ɗaya. Sanarwar ta ce a halin rayuwarta, Farfesa Effah-Attoe ta kasance mai himma da ƙwazo wadda ta bada gudummawarta ga cigaban jama'a da ma ƙasa baki ɗaya. Ologunagba ya ƙara da cewa, rasuwar Effah-Attoe ta bar wagegen giɓi a jam'iyyar…
Read More
Jam’iyyar APC ba ta da ɗan takarar Gwamna a Jihar Bayelsa – INEC

Jam’iyyar APC ba ta da ɗan takarar Gwamna a Jihar Bayelsa – INEC

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa INEC, ta fitar da sunayen ‘yan takarar gwamnan Bayelsa da Imo da aka yi wa gyaran fuska. Bisa ga lissafin da aka yi wa gyaran fuska da hukumar ta wallafa a ranar Talata, ba a saka sunayen Timipre Sylva da abokin takararsa, Joshua Maciver na jam’iyyar All Progressives Congress ba a zɓen jihar Bayelsa. Sakatariyar Hukumar, Rose Oriaran-Anthony ne ta sanya hannu a jerin sunayen. Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya ya bayar da rahoton cewa, an bar shafi na sunayen ɗan takarar Jam’iyyar APC da abokin takararsa tare…
Read More
Jam’iyyar APC a Taraba ta koka kan ƙin bai wa Mustapha muƙami a gwamnatin Tinubu

Jam’iyyar APC a Taraba ta koka kan ƙin bai wa Mustapha muƙami a gwamnatin Tinubu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Jam’iyyar APC reshen Jihar Taraba ta yi Allah-wadai da rashin shigar da tsohon Sakatare kuma mai bada shawara kan harkokin shari’a na Ƙungiyar Yaƙin Neman Zaven Tinubu/Shettima a jihar Mohammed Mustapha a cikin majalisar ministocin Shugaba Bola Tinubu. A cikin wata sanarwa da Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙaramar Hukumar Jalingo kuma shugaban ƙungiyar 16 Ciyamomi (ALGON), Bashir Bakari da wakilan shugabannin gundomomi Hon. Bello Hassan, sun bayyana damuwar su cewa ba a ɗauki Mustapha ko a saka shi a matsayin minista ba ko ba shi wani muƙami a gwamnatin TinubuSanarwar ta ci gaba da…
Read More
Ribar dimukraɗiyya sai hamdala a Zariya, amma a ƙara duba mata – Hajiya Salamatu

Ribar dimukraɗiyya sai hamdala a Zariya, amma a ƙara duba mata – Hajiya Salamatu

Daga ISAH GIDAN BAKKO a Zariya Wata fitacciyar 'yar siyasa a Jam'iyyar APC a ƙaramar hukumar birnin Zariya, Hajiya Salamatu ta bayyana yadda wasu zaɓaɓɓu ke rabon ribar dimukuraɗiyya a gundumomi goma sha uku a ko ƙaramar hukumar Zariya sai dai ta koka na yadda mata ba a yayyafa masu kamar yadda ake yayyafa wa maza ba a cewarta. Hajiya Salamatu ta ci gaba da cewa duk wani ɗan siyasa da kuma waɗanda ba ma siyasar suke yi ba, ya san jam'iyyar APC ta yi sa'ar samun wakilai guda biyu da suka san yadda al'umma suka yi amfani da damar…
Read More
Da Ɗumi-ɗumi: Kotun Ƙoli ta yi watsi da buƙatar Atiku ta neman gabatar da sabuwar hujja a kan Tinubu

Da Ɗumi-ɗumi: Kotun Ƙoli ta yi watsi da buƙatar Atiku ta neman gabatar da sabuwar hujja a kan Tinubu

Daga BASHIR ISAH Kotun Ƙoli ta yi watsi da buƙatar da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma ɗan takarar shugabancin ƙasa na Jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya gabatar wa kotun ta neman kotu ta ba shi damar gabatar mata da sabuwar hujja a kan Shugaban Ƙasa Bola Tinubu. Atiku ya buƙaci kotun da ta ba shi damar gabatar da bayanan da ya ce ya samo game da karatun da Tinubu ya ce ya yi a Jami'ar Jihar Chicago ta ƙasar Amurka. Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasar na ra'ayin cewa bayanan bogi ne Tinubu ya miƙa wa Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) a…
Read More
Kotun Ƙoli: Gobe su Atiku za su san matsayinsu

Kotun Ƙoli: Gobe su Atiku za su san matsayinsu

Daga BASHIR ISAH A ranar Alhamis ta wannan makon Kotun Ƙoli za ta yanke hukunci kan ƙarar da 'yan takarar shugabancin ƙasa ƙarƙashin jam'iyyun PDP da LP, Atiku Abubakar da Peter Obi suka shigar inda suke ƙalubalantar nasarar da Shugaba Bola Tinubu ya samu wadda Kotun Ɗaukaka Ƙara ta tabbatar masa da ita. Daraktan Yaɗa Labarai na Kotun Ƙoli, Dr Awemeri Festus Akande, shi ne ya bayyana hakan a ranar Laraba. Ya ce an ɗauki matakan tsaron da suka kamata domin tabbatar da lumana a ciki da wajen kotun. Baya ga rashin gamsuwa da nasarar Tinubu, Atiku yana kuma neman…
Read More