Siyasa

Datti Baba-Ahmed ya sha kaye a hannun Atiku a akwatin sa

Datti Baba-Ahmed ya sha kaye a hannun Atiku a akwatin sa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Datti Baba-Ahmed, ɗan takarar Mataimakin Shugaban Ƙasa na Jam’iyyar Labour Party, LP, ya sha kaye a hannun Atiku Abubakar na Jam’iyyar PDP. A rumfar zace mai lamba 021 dake Unguwar Tudun Wada, a Ƙaramar Hukumar Zariya ta Jihar Kaduna, adadin waɗanda aka tantance sun kai 272. Jam’iyyar PDP ta samu ƙuri’u 102, inda ta lashe rumfunan zaɓe, sai kuma jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da ƙuri’u 98. Jam'iyyar LP ta zo ta uku da ƙuri'u 54, yayin da NNPP ta samu ƙuri'u 11.
Read More
PDP za ta yi na’am da sakamakon zaɓe – Tambuwal

PDP za ta yi na’am da sakamakon zaɓe – Tambuwal

Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato Babban mai yekuwar neman zaɓen Atiku Abubakar kuma Gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Tambuwal, ya ce Jam'iyyar PDP za ta karɓi sakamakon zaɓe hannu bibbiyu duk yadda ya kasance. Tambuwal ya bayyana hakan ne a mahaifarsa, Tambuwal, jim kaɗa bayan kaɗa ƙuri'arsa. “Mun sani cewa duk yadda lamari ya samu ɗan Adam daga Ubangiji ne, haka shi ma shugabanci Ubangiji kan bayar da shi ga wanda ya so a kuma duk lokacin da Ya so". A cewarsa, "ganin yadda alumma suka fito zaɓe, wata manuniya ce da ke nuni da yadda jama'a suka bai wa sha'nin…
Read More
Tinubu ya sha ƙasa a rumfar Tambuwal

Tinubu ya sha ƙasa a rumfar Tambuwal

Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato Ɗan takarar shugaban ƙasa na jamiyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya sha ƙasa a rumfar zaɓen Gwamnan Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal. Tinibu ya sha ƙasar ne bayan da abokin hamayyarsa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya doke shi da ƙuri'u 250, yayin da shi kuma ya tsira da ƙuri'u 44. Tambuwal, Wanda kuma ke takarar kujerar Majalisar Dattawa ya doke Sanata Dan Baba Dambuwa na jamiyyar APC dake kan kujerar da ƙuri'u 252, yayin da Dan Baban ya samu ƙuri'u 44.
Read More
Atiku zai lashe zaɓen Shugaban Ƙasa, cewar Gwamna Bala

Atiku zai lashe zaɓen Shugaban Ƙasa, cewar Gwamna Bala

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi Gwamnan jihar Bauchi, Bala Abdulkadir Mohammed ya bayyana cewar, yana da yaƙin ɗan takarar shugabancin ƙasa na jam'iyyar su ta PDP, Atiku Abubakar zai lashe kujerar shugabancin Najeriya. Inji gwamna, "A yanzu dai ba zance komai ba, amma muna jaddada tsammani ɗan takarar mu na shugaban ƙasa, Wazirin Adamawa zai ci zaɓen nan da ikon Allah, da kuma sauran 'yan takarkari na sanatoci da 'yan majalisar tarayya. Sanata Bala Mohammed wanda yayi wannan furuci a mazabar sa ta Bakin Dutse dake garin Yelwan Duguri ta jihar Bauchi, ya kuma nuna gamsuwar sa da yadda na'urar…
Read More
Atiku ya buƙaci jami’an tattara sakamakon zaɓe su dinga shigarwa tun daga rumfuna

Atiku ya buƙaci jami’an tattara sakamakon zaɓe su dinga shigarwa tun daga rumfuna

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ɗan takarar Shugaban Ƙasa a Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya buƙaci Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu da ya umurci jami’an tattara sakamakon zaɓen na ranar Asabar da su dinga shigar da sakamakon zaɓe tun daga rumfunan zaɓe. A cikin sanarwar da mai bai wa Atiku shawara kan harkokin yaɗa labarai, Mista Paul Ibe ya sanya wa hannu, ya ce kiran ya zama wajibi "a binciki wasu gwamnonin da ke ƙoƙarin yin maguɗin zaɓe a matakin ƙananan hukumomi," inji shi
Read More
Muna fatan samun haɗin kan jama’a wajen tattara sakamakon zaɓe a Kano – INEC

Muna fatan samun haɗin kan jama’a wajen tattara sakamakon zaɓe a Kano – INEC

Daga RABIU SANUSI a Kano Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, INEC, ta buƙaci haɗin kan masu ruwa da tsaki a Jihar Kano yayin tattara sakamakon zaɓe da yafara gudana a jihar kano. Kiran ya fito ne daga bakin shugaban kwamitin tattara sakamakon zaɓe na hukumar zaɓe na jihar Kano, Farfesa Lawal Suleiman Bilbis. Tuni dai hukumar zaɓen ta jihar Kano ta fara tattara sakamakon zaɓen daga ƙananan hukumomi 44 da ke faɗin jihar. Fargesa Bilbis shi ne shugaban tattara sakamakon zaɓe a hukumar zaɓe ta jihar Kano.
Read More
Sakamakon Zaɓe: Kwankwaso ya lashe ƙananan hukumomi 9 a Kano

Sakamakon Zaɓe: Kwankwaso ya lashe ƙananan hukumomi 9 a Kano

Daga IBRAHIM Hamisu, a Kano Ɗan takarar Shugaban Ƙasa na Jam'iyyar NNPP, Dr. Rabi'u Musa Kwankwaso ya lashe ƙanan hukumomi 9, da suka haɗa da Garin Malam, Kibiya, Rimin Gado, Kura, Gazawa, Minjibir, Gabasawa, Warawa. Ga sakamakon zaɓen kamar yadda INEC ta bayyana: Garun Malam Jimillar Ƙuri'u: 74,846 Waɗanda aka tantance: 26,692 APC – 8,642LP – 169NNPP – 12,249PDP – 4,409 Rimin Gado: Adadin masu zaɓen da aka yi wa rajista: 67,128 Waɗanda aka tantance: 27,476 APC – 10,861LP – 76NNPP – 14,634PDP – 907 Kibiya: Adadin masu zaɓen da aka yi wa rajista: 77,929Waɗanda aka tantance: 28,228 APC –…
Read More
Zaɓen 2023: Abinda ya sa na kaɗa wa Tinubu ƙuri’a a filin Allah – Buhari

Zaɓen 2023: Abinda ya sa na kaɗa wa Tinubu ƙuri’a a filin Allah – Buhari

Daga AMINA YUSUF ALI Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya bayyana dalilinsa na kaɗa wa Asiwaju TInubu ɗan takarar shugaban ƙasa a jamiyyar APC ƙuri'a a bainan nasi a yayin da yake zaɓe a mahaifarsa wato Daura. Shugaban ya bayyana cewa, ba wani abu ne ya sa ya bayyana zaɓinsa ga Tinubun ba illa nuna biyayyarsa da goyon bayansa gare shi. A cewar sa, bayan ya kewaye lungu da saƙo na ƙasar nan don yin yaƙin neman zaɓe ga tsohon gwamnan na Legas, ya kamata ya cika aikinsa na jaddada goyon baya a gare shi a matsayin wanda ya fi so…
Read More
Tinubu ya lashe akwatin zaɓen el-Rufai a Kaduna

Tinubu ya lashe akwatin zaɓen el-Rufai a Kaduna

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya yi nasara a rumfar zaɓen gwamna Nasir el-Rufai na Jihar Kaduna. Tinubu ya samu ƙuri’u 173 a rumfar zaɓe mai lamba 024, Ward 07, Ungwan Sarki, Kaduna, inda ya doke ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, wanda ya samu ƙuri’u 134. Peter Obi na jam'iyyar Labour Party LP ya samu ƙuri'u uku, yayin da Rabiu Musa Kwankwaso na jam'iyyar NNPP ya samu ƙuri'u 20.
Read More
Gwamnan Gombe ya gaza kawo wa Tinubu akwatin zaɓensa

Gwamnan Gombe ya gaza kawo wa Tinubu akwatin zaɓensa

Daga Daga MAHDI M. MUHAMMAD Gwamnan Jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya, ya kasa kawo wa Tinubu akwatinsa zaɓensa, inda ya sha kaye a hannun jam'iyyar PDP. A sakamakon zaɓen da aka sanar da jama'a da dama, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya samu ƙuri'u 215 inda ya doke ɗan takarar jam'iyyar APC, wanda ya samu ƙuri'u 186 a jam'iyyar. Da yake bayyana sakamakon zaɓen, jami’in zaɓe (PO) na mazaɓar Yahaya Umar 010 da ke makarantar gwamnati ta Gombe, Misheal Thomas ya bayyana cewa jam’iyyar NNPP ta samu ƙuri’u 10 ne kacal yayin da LP ta samu…
Read More