Siyasa

Mai juna-biyu ta mutu a wajen zaɓe a Zamfara

Mai juna-biyu ta mutu a wajen zaɓe a Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau. Wata mata mai juna-biyu mai suna Shamsiya Ibrahim ta yanke jiki ta faɗi matacciya a yayin da take jiran layin kaɗa ƙuri'a yayin zaɓen Shugaban Ƙasa da na 'yan Majalisar Tarayya. Wannan al'amari ya auku ne ranar Asabar a yankin ƙaramar hukumar Tsafe da ke Jihar. Blueprint Manhaja ta tattaro cewa bayan da matar ta yanke jiki ta faɗi, an garzaya da ita Babban Asibitin Tsafe inda aka tabbatar da rasuwarta. Shamsiya ta yi tattaki ne daga yankin Kotorkoshi da ke Ƙaramar Hukumar Bunguɗu zuwa garin Tsafe mai nisan kimanin kilomita 50 don kaɗa ƙuri’arta.…
Read More
Ban taɓa ganin zaɓe cikin kwanciyar hankali ba sai a wannan karon – Sanata Barau

Ban taɓa ganin zaɓe cikin kwanciyar hankali ba sai a wannan karon – Sanata Barau

Daga RABIU SANUSI a Kano Ɗan takarar sanata a Kano ta Arewa ƙarƙashin jam'iyyar APC, Hon. Barau I. Jibrin (maliya), ya bayyana cewa bai taɓa ganin zaɓe cikin kwanciyar hankali makamancin wannan ba. Barau ya bayyana haka ne yayin zantawa da manema labarai jim kaɗan bayan kaɗa kuri'arsa a mazaɓar sa ranar Asabar. "Ina ganin zan samu lashe wannan zaɓe da tazara mai yawa tsakani na da sauran abokan karawa ta," in ji Barau. Kazalika, a yayin gudanar da zaɓen an ji al'umma daga lungu da saƙo wajen gudanar da zaɓen suna kiran sai "Maliyan Kanawa" musamman yadda mutane suka…
Read More
Yadda ɗan takarar gwamnan Bauchi a jam’iyyar APC da matarsa, Ministar Jinƙai suka kaɗa ƙuri’unsu

Yadda ɗan takarar gwamnan Bauchi a jam’iyyar APC da matarsa, Ministar Jinƙai suka kaɗa ƙuri’unsu

Daga Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ɗan takarar gwamna na jam’iyyar APC a Jihar Bauchi, kuma tsohon shugaban sojin sama, Sadique Abubakar, tare da matarsa, Ministar Harkokin Jinƙai da Cigaban Jama’a, Sadiya Farouk, sun kaɗa ƙuri’unsu a Zirami Ƙofar Fada 001, a Ƙaramar Hukumar Giade a yankin jihar. Abubakar, a lokacin da yake zantawa da ’yan jarida ya yaba wa Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) kan inganta harkokin zaɓe da kuma ɓullo da tsarin tantance masu kaɗa ƙuri’a na BVAS. Ya ce, “Ya zuwa yanzu, abubuwan sun inganta a yankunan da na ziyarta. Na yi zaɓe a Zirami, Ƙofar Fada Ward…
Read More
Dalilin da ya sa kayan zaɓe suka makara a wasu mazaɓun — INEC

Dalilin da ya sa kayan zaɓe suka makara a wasu mazaɓun — INEC

Daga AMINA YUSUF ALI Chief Emmanuel Chike, wani ma'aikacin INEC ya bayyana cewa, rashin soma kasafta kayan aikin zaɓe a kan kari tun a ranar Juma'a shi ne ya yi sanadiyyar samun tsaiko wajen rarraba su ga mazaɓu a ranar zaɓe ranar Asabar. Chike, jamiin rajista (RAC) a garin Fatakwal Ƙaramar Hukumar Fatakwal ya bayyana wa 'yan jaridu a ranar asabar cewa, sai ƙarfe 6 na yammacin Juma'a sannan hukumar INEC ta soma kasafta kayan aikin da za a rarraba a mazaɓu. Haka kuma a cewar sa, wasu jami'an ma sai ranar Asabar ɗin da sassafe wato ranar zaɓen sannan…
Read More
Daraktan yaƙin neman zaɓen Obi ya sha kayi a garinsa

Daraktan yaƙin neman zaɓen Obi ya sha kayi a garinsa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Darakta Janar na yaƙin neman zaɓen ɗan takarar Shugaban Ƙasa na Jam’iyyar Labour, Akin Osuntokun, ya faɗi zaɓe a ƙaramar hukumarsa ta haihuwa. Jam’iyyar APC mai mulki a ranar Asabar, 25 ga watan Fabrairu, 2023, ta lashe zaɓen Shugaban Ƙasa da gagarumin rinjaye a Ekiti ta Yamma. Ɗan takarar Shugaban Ƙasa na Jam’iyyar APC, Bola Tinubu ya doke takwaransa na Jam’iyyar LP Peter Obi, wanda ya zo na uku. A sakamakon da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa INEC, jami’in tattara bayanan ƙananan hukumomi ya bayyana, Jam’iyyar APC ta lashe dukkan gundumomi 11…
Read More
Shugaban APC na Ƙasa da Kakakin Majalisar Wakilai sun sha kaye a rumfunan zaɓensu

Shugaban APC na Ƙasa da Kakakin Majalisar Wakilai sun sha kaye a rumfunan zaɓensu

Daga SANI AHMAD GIWA abuja Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya sha kaye a rumfarsa ta gundumar Angwan Rimi, GRA A1, da ke ofishin LERCEST da ke garin Keffi a Jihar Nasarawa, a zaɓen Shugaban Ƙasa da aka gudanar ranar Asabar, inda Jam’iyyar Labour ta yi nasara. Peter Obi na Jam’iyyar Labour ne ya yi nasara a akwatin da ƙuri’u 132 yayin da APC ta zo ta biyu da ƙuri’u 85. Wannan lamari dai na zuwa ne jim kaɗan bayan da Kakakin Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila ya sha kaye a hannun Jam'iyyar Labour shi ma. A rumfar…
Read More
Gwamnan Kwara ya kaɗa ƙuri’a, ya nuna damuwa kan na’urar BVAS

Gwamnan Kwara ya kaɗa ƙuri’a, ya nuna damuwa kan na’urar BVAS

Daga WAKILINMU Bayan jinkirin da aka samu na zuwan kayan aikin zaɓe a mazaɓarsa, a ƙarshe Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq na Jihar Kwara ya samu kaɗa ƙuri'arsa. Gwamnan ya jefa ƙuri'ar tasa ce a mazaɓarsa mai lamba 004 da ke gundumar Adewole a Ilorin ta yamma. Ya nuna damuwarsa kan ƙalubalen da aka fuskanta na rashin aikin na'urar BVAS a wasu sassan jihar. Kana ya yaba wa ƙoƙarin jami'an tsaro da kuma yadda jama'a suka fito a jihar don jefa ƙuri'arsu. A ƙarshe, Gwamnan ya bayyana yaƙininsa na cewa ko shakka babu APC za ta yi nasara.
Read More
Da Ɗumi-ɗumi: Atiku ya lashe zaɓe a rumfar Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmed Lawan a Yobe

Da Ɗumi-ɗumi: Atiku ya lashe zaɓe a rumfar Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmed Lawan a Yobe

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN a Damaturu Sakamakon zaɓen shugaban ƙasa, a rumfar da Shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya, Sanata Ahmed Lawan ya jefa ƙuri'arsa, ya nuna jam'iyyar PDP tare da dan takararta na shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar ya doke abokin takarar sa a jam'iyyar APC, Bota Ahmed Tinubu, da tazara mai yawa. Rumfar zaɓen wadda take a makarantar Firamaren Katuzu mai lamba 001B, inda sakamakon ya nuna dan takarar shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu na APC ya samu kuri'u 107, yayin da Sanata Rabi'u Kwankwaso na NNPC ya samu ƙuri'u 41, sai Alhaji Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP mai ƙuri'u 186.…
Read More
Wasu ‘yan takarar siyasar Nijeriya da suka rasa rayukansu gab da zaɓen 2023

Wasu ‘yan takarar siyasar Nijeriya da suka rasa rayukansu gab da zaɓen 2023

Daga AMINA YUSUF Wasu daga cikin waɗannan 'yan takarar ana gab da zaɓen 2023 'yan bindiga suka halaka su, wasu daga ciki kuma suka rasu ta hanyar wasu dalilan. Halin rashin tsaron da ƙasar nan ya yi sanadiyyar kisan ba wai 'yan takarar kaɗai ba har ma da masu tsaron lafiyarsu. Haka ma magoya bayansu sun sha shiga irin wannan ibtila'in a wannan kakar zaɓen. Rahotanni dai suna nuna zargin cewa, waɗannan 'yan siyasa vangaren da suke adawa ne da su suke kashe su saboda suna ganinsu a matsayin barazana ga siyasarsu. Duk kuwa da cewa, a cikin 'yan kwanakin…
Read More