Siyasa

Wasu ‘yan takarar siyasar Nijeriya da suka rasa rayukansu gab da zaɓen 2023

Wasu ‘yan takarar siyasar Nijeriya da suka rasa rayukansu gab da zaɓen 2023

Daga AMINA YUSUF Wasu daga cikin waɗannan 'yan takarar ana gab da zaɓen 2023 'yan bindiga suka halaka su, wasu daga ciki kuma suka rasu ta hanyar wasu dalilan. Halin rashin tsaron da ƙasar nan ya yi sanadiyyar kisan ba wai 'yan takarar kaɗai ba har ma da masu tsaron lafiyarsu. Haka ma magoya bayansu sun sha shiga irin wannan ibtila'in a wannan kakar zaɓen. Rahotanni dai suna nuna zargin cewa, waɗannan 'yan siyasa vangaren da suke adawa ne da su suke kashe su saboda suna ganinsu a matsayin barazana ga siyasarsu. Duk kuwa da cewa, a cikin 'yan kwanakin…
Read More
Yadda Ganduje ya daidaita sahu wajen kaɗa ƙuri’a, ya yaba wa na’urar BVAS

Yadda Ganduje ya daidaita sahu wajen kaɗa ƙuri’a, ya yaba wa na’urar BVAS

Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano Kyamarar wakilinmu a Kano ta samu sa'ar ɗaukar Gwamnan Jihar Kano, Dokta Abdullahi Umar Ganduje, a lokacin da ya daidaita sahu ya bi layi kamar sauran jama'a wajen kaɗa ƙuri'arsa. Ganduje ya jefa ƙuri'ar tasa ce a mazaɓarsa ta Cikin-gari mai lambar akwatu 008 da ke garin Ganduje, Ƙaramar Hukumar Dawakin-Tofa, Kano. Ganduje a wajen zaɓe Gwamnan ya yaba tare da jinjina wa hukumar zaɓe ta INEC bisa matakin yin amfani da na'urar BVAS wajen tantance masu zaɓe. Ya ce, amfani da na'urar zai taimaka wajen damun sahihin zaɓe a Nijeriya.
Read More
Da ɗumi-ɗumi: INEC ta ɗage zaɓen kujerar Sanatan Enugu ta gabas

Da ɗumi-ɗumi: INEC ta ɗage zaɓen kujerar Sanatan Enugu ta gabas

Daga AMINA YUSUF ALI Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, (INEC), ta sanar da ɗage zaɓen kujerar Sanata na Enugu ta gabas zuwa 11 ga watan Maris na wannan shekarar. Hakan ya biyo bayan kisan ɗan takarar wannan kujerar na jamiyyar LP, Barista Oyibo Chukwu, wanda aka yi a ranar Laraba, 22 ga Fabrairun 2023. Shugaban hukumar INEC, Mahmood Yakubu, shi ne ya bayyana haka a yayin taron 'yan jarida ɗazu a Abuja. A cewar sa, wannan sanarwa ta dogara ne da dokar zaɓe ta kundin mulkin ƙasar nan da ta ba wa jamiyyar da ta rasa ɗan takararta…
Read More
Zargin ƙulla maguɗin zaɓe: Atiku ya fayyace komai

Zargin ƙulla maguɗin zaɓe: Atiku ya fayyace komai

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya mayar da martani ga wani faifan murya da aka yi masa na zargin cewa yana shirin yin maguɗi a ranar Asabar, 25 ga Fabrairu, 2023, a zaɓen shugaban ƙasa. An zargi abokin takarar Atiku kuma gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa, tare da shugaban jam'iyyar PDP na yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa (PDPPCC), da gwamnan jihar Sakkwato, Aminu Tambuwal. Da yake mayar da martani, kakakin jam’iyyar PDP, Phrank Shuaibu, a wata sanarwa a ranar Juma’a, ya ce aikin jam’iyyun adawa ne. Sanarwar ta ce, “mun yi gargaɗi…
Read More
Zaɓen 2023: An zo wajen!

Zaɓen 2023: An zo wajen!

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Da gani ko da duba agogo an zo wajen gudanar da babban zaɓen Nijeriya na 2023. Duk wasu shirye-shirye na wannan zaɓe sun kammala. Ko ma dai yaya lamarin zai kasance a tsarin zaɓen Nijeriya da a kan gudanar bayan shekaru 4 ko a ce yayin da wanda ya ke kan kujera ya cika shekaru 4 kan mulki zai sauka a sanadiyyar faɗuwa zave ko kuma kammala wa’adi biyu na tsawon shekaru 8. Shugaban Nijeriya da ke kan gado Muhammadu Buhari zai kammala wa’adin mulkinsa a ranar 29 ga watan mayu mai zuwa. Don haka za…
Read More
Zaɓe: Tarihi ya maimaita  kansa a Kebbi

Zaɓe: Tarihi ya maimaita  kansa a Kebbi

Daga JAMIL GULMA a Kebbi  Tun lokacin da iskar guguwar siyasa ta soma kaɗawa dai 'yar manuniya ta nuna tarihi zai maimaita kansa bisa irin cin kashin da aka yi wa jam'iyyar PDP a lokacin mulkin shugaban Goodluck Ebele Jonathan. Jihar Kebbi ma bisa ga dukkan alamu ta bi sahun waɗansu jihohi inda a kullum safiya ta Allah al'umma sai tururuwa suke yi suna canza sheƙa daga jam'iyyar APC mai mulki zuwa PDP ta adawa. Alhaji Ibrahim Kunne Gulma wani jigo ne a jam'iyyar APC da babban hadimin tsohon shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa Alhaji Bilyaminu Bawale Sardaunan matasan…
Read More
Yadda zaɓen 2023 ya sha bamban da sauran

Yadda zaɓen 2023 ya sha bamban da sauran

*Addinanci, ƙabilnci da ɓangaranci ba baqi ne a siyasar Nijeriya ba!*Shin za a iya zuwa zagaye na biyu? Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja A gobe Asabar ne za a gudanar da Babban Zaɓe a Nijeriya bayan shafe kusan shekaru huɗu na zango na biyu da shugaba mai ci, Muhammadu Buhari, ya yi a kan kujerar mulkin ƙasar. Kowane zaɓe ya kan zo da yanayinsa kuma ya kan sha bamban da na bayansa. Siyasar addinanci da ɓangaranci ko ƙabilanci ba baƙin abubuwa ba ne a Nijeriya. Don haka ba su daga cikin abubuwan da zaɓen 2023 ya bambanta da na…
Read More
Buhari ya isa Katsina domin kaɗa ƙuri’a gobe

Buhari ya isa Katsina domin kaɗa ƙuri’a gobe

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya isa Jihar Katsina, inda daga nan ne zai zarce zuwa Daura, mahaifarsa, domin halartar zaɓen Shugaban Ƙasa da na ‘yan majalisun tarayya da za a yi gobe Asabar.Jirgin shugaban ya sauka a filin jirgin saman Umar Musa Yar’Adua da misalin ƙarfe 4:40 na yammacin jiya Alhamis, 23 ga Fabrairu, 2023. A gobe Asabar ne ake sa ran zai kaɗa ƙuri’arsa ga ‘yan takarar da yake so a Daura. Kafin ya bar Abuja zuwa Katsina, a ranar Alhamis ɗin da ta gabata, Buhari ya kira taron majalisar tsaro, inda ya…
Read More
2023: Kano ta zarce ko’ina yawan wakilan jam’iyyu

2023: Kano ta zarce ko’ina yawan wakilan jam’iyyu

•Yayin da APC, PDP da NNPP suka tura sama da wakilai 1.5 Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa INEC, a ranar Litinin ta fitar da adadin wakilan jam'iyyu a rumfunan zaɓe da wajen tattara sakamako kamar yadda jam’iyyu suka miqa wa INEC sunayensu don babban zaɓen 2023. Jaridar News Point Nigeria ta ruwaito cewa, jimillar wakilan rumfunan zaɓe na jam'iyya 1,574,301 da kuma wakilai 68,057 ne jam'iyyun siyasar ƙasar suka miƙa wa INEC. A taƙaice dai, Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki ta tura wakilai 176,223 rumfunan zaɓe a duk faɗin ƙasar;…
Read More