03
Apr
Daga AISHA ASAS Kankana na ɗaya daga cikin 'ya'yan itace da ke da matuƙar tasiri a gyaran fata da kuma kawar da cututtukan fata masu dama. Tana ɗauke da sinadaran da ke gusar da maiƙon da ke fita a hanyoyin fitar gumi, wanda idan ya yawaita zai iya haifar da fesowar qananan ƙuraje. Kankana na taka muhimmiyar rawa wajen gyara fatar da ta ke yawan yankwanewa, idan aka markaɗe ta (ba tare da an zuba mata ruwa ko kaɗan ba, kuma za a haɗe ne har 'ya'anta) aka zuba mata zuma kaɗan, ana shafawa a inda matsalar ta ke sau…
