Wasanni

Arteta na takarar zama gwarzon koci a Firimiya na watan Agusta

Arteta na takarar zama gwarzon koci a Firimiya na watan Agusta

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Mikel Arteta na takarar gwarzon koci a Firimiya na watan Agusta, bayan da ya ja ragamar Arsenal wasa huɗu ba tare da an doke ƙungiyar ba. Kocin ya doke Nottingham Forest da Crystal Palace da yin 2-2 da Fulham a dai gasar ta firimiya da haɗa maki bakwai a watan na Agusta. Wannan ƙwazon na koci ya sa shi cikin koci biyar da ke takara kocin da ba kamarsa a watan na jiya. Mikel, wanda ya lashe kyauta huɗu ta gwarzon koci a firimiya a bara na takara tare da Pep Guardiola na Manchester City, bayan…
Read More
Roma da kammala ƙulla yarjejeniyar karvar aron Lukaku daga Chelsea

Roma da kammala ƙulla yarjejeniyar karvar aron Lukaku daga Chelsea

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa ta Roma ta kammala ƙulla yarjejeniyar karɓar aron Romelu Lukaku daga Chelsea wanda zai shafe tsawon kakar bana ya na takawa ƙungiyar mai doka gasar Serie A leda. Roma ƙarƙashin jagorancin Jose Mourinho ta bi sahun manyan ƙungiyoyin Turai da suka miƙa buƙatar karvar aron Lukaku ne bayan da Mauricio Pochettino ya bayyana cewa ɗan wasan baya sahun waɗanda zai yi amfani da su a wannan kaka. Lukaku ɗan Belgium mai shekaru 30 da kanshi ya zabi komawa Roma fiye da Inter Milan ƙungiyar da ya kai wasan ƙarshe na gasar kofin zakarun…
Read More
Yadda aka raba jaddawalin Gasar Zakarun Turai

Yadda aka raba jaddawalin Gasar Zakarun Turai

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Jaddawalin gasar cin Kofin Zakarun Turai: Man United na rukuni ɗaya da Bayern Munich, Madrid za ta fuskanci Napoli An kammala fitar da jadawlin gasar Zakarun Turai na bana, inda ƙungiyoyi guda 32 suka san rukunnen da suka faɗa kuma da ƙungiyoyin da za su fafata da su. Man United za su kara da Harry Kane bayan an haɗa su da zakarun Bundesliga yayin da Arsenal ta tashi kunnen doki. Manchester United ta yi kunnen doki sosai bayan dawowarta gasar zakarun Turai kuma za ta kara da Bayern Munich a rukunin A da kuma Copenhagen da…
Read More
Shugabannin ƙwallon ƙafar Sifaniya sun buƙaci Rubiales ya yi murabus

Shugabannin ƙwallon ƙafar Sifaniya sun buƙaci Rubiales ya yi murabus

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Shugabannin hukumomin ƙwallon ƙafa na Sifaniya sun yi kira ga shugaban hukumar ƙwallon ƙafar ƙasar, Luis Rubiales da ya gaggauta yin murabus bayan ya sumbaci 'yar wasa Jenni Hermoso. Rubiales, mai shekaru 46, ya sha suka sosai bayan da lamarin ya faru bayan kammala wasan ƙarshe na gasar kofin duniya na mata a da Sifaniya ta lashe. Hermoso, mai shekaru 33, ta ce ba ta amince da sumbar da Rubiales ya yi mata ba. Tun da farko, masu gabatar da ƙara na Sifaniya sun ƙaddamar da bincike na share fage kan ko lamarin ya kai wani…
Read More
Real Madrid ta fasa sayen Mbappe – Ancelotti

Real Madrid ta fasa sayen Mbappe – Ancelotti

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Kocin Real Madrid, Carlo Ancelotti ya ce, ba zai sayi ɗan wasan gaba Kylian Mbappe daga Paris St-Germain a bana ba. Mbappe, ɗan shekara 24 ya zuwa yanzu ya ƙi rattaba hannu a kan kwantiragi da PSG, lamarin da ya sa ake raɗe-raɗin cewa zai koma ƙungiyar ta La Liga. Ana tunanin cewa PSG a shirye take ta sayar da kyaftin ɗin na Faransa, maimakon yin kasadar rasa shi kyauta idan kwantiraginsa ya ƙare a shekara mai zuwa. Da aka tambaye shi game da yarjejeniyar Mbappe, Ancelotti ya ce "A'a, na yanke hukunci kashi 100." Mbappe…
Read More
Shugaban Hukumar Ƙwallon Ƙafar Sifaniya ya nemi afuwa bayan sumbatar ‘yar wasa

Shugaban Hukumar Ƙwallon Ƙafar Sifaniya ya nemi afuwa bayan sumbatar ‘yar wasa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Fira Ministan Spain Pedro Sanchez ya caccaki shugaban Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Ƙasar Sifaniya, Luis Rubiales, kan yadda ya sumbaci 'yar wasan da ta lashe gasar kofin duniya ta mata Jenni Hermoso. A cewar Fira Ministan, bayar da haƙuri kan lamarin kawai ba zai isa ba idan aka yi la'akari da girman abin da ya faru. Shugaban hukumar ƙwallon ƙafar ƙasar Sifaniya, Luis Rubiales ya nemi afuwa sakamakon sumbatar ’yar wasan tawagar ƙwallon ƙafar mata ta ƙasar, Jenni Hermoso da ya yi a leɓe, bayan da suka lashe kofin duniya ta mata da aka kamala a…
Read More
Deco ya zama sabon daraktan wasannin Barcelona

Deco ya zama sabon daraktan wasannin Barcelona

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Tsohon ɗan wasan Barcelona Deco ya zama sabon daraktan wasanni a ƙungiyar Ɗan ƙasar Portugal haifaffen Brazil, mai shekara 45, ya rattaba hannu kan kwantiragin shekara uku a Nou Camp. Deco ya fara komawa Barcelona ne daga Porto a shekara ta 2004 kuma ya lashe gasar La Liga sau biyu a kakar wasanni hudu, da kuma gasar Zakarun Turai a shekarar 2006. Barca ta ce Deco ne zai jagoranci sabuwar aƙidar wasansu kuma zai yi aiki tare da koci Xavi da sauran ma su taimaka masa. Ƙungiyar ta ce, tana shirin yi wa ɓangaren gudarwarta garambawul,…
Read More
Taiwo Awoniyi: Yadda birkila ɗan Nijeriya ya koma buga Firimiyar Ingila

Taiwo Awoniyi: Yadda birkila ɗan Nijeriya ya koma buga Firimiyar Ingila

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Lokacin da koci Steve Cooper ke ƙoƙarin gina harsashin Nottingham Forest don tsira a gasar firimiya, ya yi duban tsanaki inda ya ga ya dace ya ɗauko ɗan wasan farko wanda ya kasance tsohon mai aikin birkila. Kuma tabbas Taiwo Awoniyi ya saka masa, yayin da ɗan Nijeriyar ya taimaka wurin nasarar da Forest ta samu na farko a kakar bara, wadda ta doke West Ham 1-0 da cin Arsenal 1-0, hakan ya sa ta ci gaba da zama a gasar Firimiya a watan Mayu. Hakan ya zo ne saura mako ɗaya a ƙarƙare wasannin bara,…
Read More
Wolves ta naɗa Gary O’Neil sabon kocinta

Wolves ta naɗa Gary O’Neil sabon kocinta

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Wolverhampton ta sanar da naɗa tsohon kocin Bournemouth, Garry O'Neil, a matsayin wanda zai horar da ita. Tuni ya amince da kwantiragin kaka uku, ya kuma maye gurbin Julen Lopetegui. An sanar da raba gari tsakanin ƙungiyar da Lopetegi a Molineu ranar Talata, kwana uku kafin fara kakar firimiya ta 2023/24. O'Neil ya ja ragamar Bournemouth zuwa mataki na 15 a teburin firimiya a bara, daga baya ta kore shi ranar 19 ga watan Yuni. Mai shekara 40, shi ne kocin Wolves na hudu cikin shekara biyu. Zai fara aiki ranar Litinin, lokacin da Wolves za…
Read More
Courtois zai yi jinya mai tsawo a Real Madrid

Courtois zai yi jinya mai tsawo a Real Madrid

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Mai tsaron ragar Real Madrid, Thibaut Courtois zai yi jinya mai tsawo a kakar bana, bayan da ya ji rauni a gwiwar ƙafarsa ta hagu. A ’yan kwanaki masu zuwa likitoci za su yi wa golan tawagar Belgium, mai shekara 31 tiyata, daga baya a fayyace kwanakin jinyar da zai yi. Courtois, wanda aka zava mai tsaron raga mafi fice a duniya a bikin kyautar Ballon d'Or a bara, ya lashe La Liga biyu tun bayan da ya koma Real a 2018. Ya buga wa Real wasa 230, wadda za ta kece raini da Athletic Bilbao…
Read More