Wasanni

Barcelona da Chelsea na rububin ƙulla yarjejeniya da Neymar

Barcelona da Chelsea na rububin ƙulla yarjejeniya da Neymar

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Makomar Neymar idan har ya rabu da PSG na cigaba da kasancewa cikin rashin tabbas a daidai lokacin da ɗan wasan tare da ƙungiyar ta sa suka amince da Shirin rabuwar nan ba da jimawa ba. Sai dai mai yiwuwa burin ƙungiyoyin Barcelona da Chelsea waɗanda ke son ƙulla yarjejeniya da ɗan wasan ya gaza cika, saboda ƙalubalen da kowannensu ke fuskanta. A ɓangaren Chelsea, a yayin da ta kasance ƙungiyar da za fi dacewa da samun sauƙin sayen Neymar, ba lallai bane ɗan wasan ya amince da tayin komawa gare ta, la’akari da cewar ba…
Read More
Mourinho ya musanta yunƙurin tunzura shugabannin Roma

Mourinho ya musanta yunƙurin tunzura shugabannin Roma

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Kocin Roma, Jose Mourinho ya musanta yunƙurin tunzura shugabannin ƙungiyar da wani hoto a shafinsa na Instagram amma ya ce abubuwa ba su daidaita ba. A hoton ana iya ganin Mourinho mai shekaru 60 da ma’aikatansa suna rungumar wani abin da ba a gani bayan Roma ta gaza ɗauko sabon ɗan wasan da zai maye gurbin Tammy Abraham wanda ke ɗauke da rauni. An saka hoton ne a ƙarshen atisayen da ƙungiyar Roma ta yi a ƙasar Portugal mako ɗaya da ya wuce. An ɗauke ɗan wasan gaban Ingila Abraham, mai shekara 25, jim kaɗan bayan…
Read More
Wolves ta sallami kocinta Lopetegui

Wolves ta sallami kocinta Lopetegui

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Kocin Wolves Julen Lopetegui ya bar ƙungiyar, inda tsohon kocin Bournemouth Gary O'Neil zai maye gurbinsa. Wolves ta ce, ta daɗe da fahimtar cewa Lopetegui, mai shekaru 56, yana son barin ƙungiyar. Ƙungiyar ta kuma ce dukkan vangarorin biyu sun amince da savanin ra'ayi kan wasu batutuwa kuma sun amince cewa kawo ƙarshen kwantiraginsa cikin aminci shi ne mafita mafi kyau". Wolves ta sanar da barin kocin ɗan Sifaniya kwanaki uku kafin a fara gasar firimiya, inda za su kara da Manchester United ranar Litinin. Kulob ɗin ya ce, "an ci gaba da tattaunawa a cikin…
Read More
FIFA za ta biya kuɗin fafatawa a kofin duniya ga asusun ’yan wasa kai tsaye

FIFA za ta biya kuɗin fafatawa a kofin duniya ga asusun ’yan wasa kai tsaye

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Hukumar Ƙwallon Ƙafar Duniya (FIFA) ta sanar da aniyarta ta biyan kuɗaɗen da ake bai wa duk tawagar da aka dama da ita a gasar kofin duniya ta Australia da New Zeland kai tsaye ga asusun ajiyar ’yan wasan maimakon ta biya hukumar ƙwallon ƙafar ƙasashensu. Ta shafi tawagar ƙwallon ƙafar mata ta Nijeriya, Super Falcons. Tun da farko an jiyo kocin tawagar Falcons ɗin, Randy Waldrum yana cewa akwai wasu ’yan wasan tawagar da har yanzu suke bin haƙƙoƙinsu tsawon shekaru biyu. Wannan lamari dai ya janyo tada jijiyoyin wuya, inda har ya kusan yin…
Read More
PSG za ta biya Mbappe yuro miliyan 60 a matsayin tukwicin riƙe shi

PSG za ta biya Mbappe yuro miliyan 60 a matsayin tukwicin riƙe shi

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Rahotanni daga birnin Paris na cewa akwai yiwuwar PSG za ta biya ɗan wasanta Kylian Mbappe kuɗaɗen da yawansu ya kai yuro miliyan 60 a matsayin tukwicin yabawa da biyayya ko amintakar da ke tsakaninsu. Bayanan sun ce ƙungiyar ta París Saint Germaine za ta biya tauraron na ta maƙudan kuɗaɗen ne, muddin bai raba gari da ita har zuwa ranar 1 ga watan Agusta, duk da cewar dangantakar da ke tsakaninsu ta yi rauni matuƙa, biyo bayan ƙin tsawaita yarjejeniyarsa da ya yi da ke shirin karewa a 2024. Yanzu haka dai ƙungiyoyi da dama…
Read More
Abdu Maikaba ya zama sabon kocin Kno Pillars

Abdu Maikaba ya zama sabon kocin Kno Pillars

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa ta Kano Pillars ta naɗa Abdullahi Maikaba a matsayin sabon kocinta. Maikaba ya rattaba hannu kan kwangilar shekara biyu da kungiyar da ake kira "Sai Masu gida" daga kakar 2023/2024 zuwa 2024/2025. Kocin zai yi aiki tare da Abubakar Abubakar da ake kira Senior da Ahmad Garba Yaro Yaro da Gambo Muhammad da kuma Auwalu Abbas a matsayin mai horar da masu tsaron gida. Da yake ƙaddamar da kocin a ofishinsa, mataimakin gwamnan jihar Kano, Kwamared Aminu AbdulSalam Gwarzo, ya buƙace shi da ya zage damtse domin farfado da martabar ƙungiyar. Mataimakin gwamnan,…
Read More
Napoli ta yi wa Osimhen tayin Naira biliyan shida duk shekara

Napoli ta yi wa Osimhen tayin Naira biliyan shida duk shekara

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Zakarar gasar Seria A a kakar da ta gabata Napoli, ta yi wa ɗan wasan gabatanta Victor Osimhen tayin kwantiragin shekaru biyu, inda za ta riƙa biyan shi Yuro miliyan 6 da dubu ɗari biyar kwatankwacin Naira biliyan shiga da miliyan ɗari biyar a duk shekara. Ɗan wasan da ke da ragowar kwantaragin shekaru biyu da ƙungiyar, ya buƙaci ta riƙa biyan sa Yuro miliyan 7 a duk shekara. Osimehen mai shekaru 24 ya taimakawa Napoli wajen lashe gasar Seria A karon farko a cikin shekaru 33, inda ya zura ƙwallaye 26 a cikin wasanni 32…
Read More
An gaza biyan ’yan wasa mata kuɗaɗensu gabanin fara gasar kofin duniya

An gaza biyan ’yan wasa mata kuɗaɗensu gabanin fara gasar kofin duniya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Shugaban Hukumar Kula da Ƙwallon Ƙafa ta Duniya (FIFA) Gianni Infantino, ya ce babu tabbacin hukumomin ƙwallon ƙafar ƙasashe da suka sami gurbi a gasar lashe kofin duniya ta mata da aka fara a ranar Alhamis, da ƙasashen Australia da New Zealand za su ɗauki nauyi, za su iya kammala rabawa ’yan wasansu kuɗaɗen da ya kamata a ba su. Kowace 'yar wasa da za ta fafata a gasar za ta samu dala dubu 30, wanda a baya hukumar ta ce za ta tura musu kuɗinsu kai tsaye, ba sai ya bi ta hannun hukumomin ƙasashensu…
Read More
Riyad Mahraz na daf da komawa Al Ahli ta Saudiyya

Riyad Mahraz na daf da komawa Al Ahli ta Saudiyya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa ta Manchester city ta amince da tayin fan milyan 30 a kan ɗan wasanta Riyad Mahrez da ƙungiyar Al Ahli ta saudiyya ta yi. Ɗan wasan mai shekara 32 tuni city ta ba shi izinin ya zauna karya shiga tawagar ’yan wasan ƙungiyar da suke atisaye a nahiyar Asia. Yanzu haka ya rage ga Mahrez ya tattauna da Al Ahli akan batun albashin sa. Rahotanni sun kwarmata cewa tuni ya amince da kwantaragin shekaru uku a ƙungiyar dake birnin Jeddah. Shekaru biyu suka rage kwantaragin ɗan wasan ya ƙare a Etihad, sai dai…
Read More
Hada-hadar kasuwar ’yan wasan ƙwallon ƙafa

Hada-hadar kasuwar ’yan wasan ƙwallon ƙafa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Everton na son ɗan wasan Faransa Moussa Dembele, mai shekara 27, da kuma mai bugawa Leicester, Jamie Vardy, mai shekara 36. Newcastle na ci gaba da tattaunawa da Leicester kan ɗan wasanta na gefe Harvey Barnes, mai shekara 25, kan fan miliyan £30. Ɗan wasan tsakiya a Nice da Wales Aaron Ramsey, mai shekara 32, ya samu tayi mai gwavi daga Saudiyya. Mai buga tsakiya a Tottenham da Denmark Pierre-Emile Hojbjerg, mai shekara 27, ya kasance matashin da Atletico Madrid ta jima tana zawarci. Chelsea a shirye take ta sayar da Trevoh Chalobah, mai shekara 24,…
Read More