Wasanni

Ahmed Musa ya jefa Ronaldo da Al-Nassr cikin matsala

Ahmed Musa ya jefa Ronaldo da Al-Nassr cikin matsala

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Duniya (FIFA) ta haramta wa Al-Nassr rajistar sabbin ’yan wasa saboda rashin biyan wasu kuɗaɗen da Leicester City ke bin ta a wani ɓangare na yarjejeniyar Ahmed Musa. Al-Nassr ya sayi Cristiano Ronaldo ne a watan Janairun 2023 amma FIFA ta dakatar da ita daga sake yin rajistar sabbin ’yan wasa sakamakon taqaddama ƙungiyar Leicester. Hakan ya faru ne sakamakon gazawar kulob ɗin Saudiyyar na kasa biyan ƙungiyar Leicester ƙarin kuɗaɗe dangane da yarjejeniyar da ta yi da ɗan wasan Nijeriya, Ahmad Musa. Tsohon ɗan wasan gaban CSKA Moscow ya koma Foxes…
Read More
Editan Jaridar Blueprint ya zama Sakataren SWAN na ƙasa

Editan Jaridar Blueprint ya zama Sakataren SWAN na ƙasa

An rantsar da Eiditan Jaridar Blueprint na intanet, Amb. Ikenna Okonkwo, a matsayin Sakataren Ƙungiyar Marubuta Labaran Wasanni ta Nijeriya. Amb. Okonkwo ya gaji wannan matsayi ne a wajen Mr. Jude Opara bayan da ya tsaya takarar neman muƙamin ba tare da hamayya ba. Haka nan, Mr. Isaiah Benjamin na Jaridar Leadership shi ne wanda aka rantsar a matsayin shugaban ƙungiyar SWAN na ƙasa bayan babban taron da ƙungiyar ta gudanar a ranar Alhamis, 13 ga Yulin 2023.
Read More
Everton ta ɗauki Ashley Young

Everton ta ɗauki Ashley Young

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Everton ta ƙulla yarjejeniya da Ashley Young kan kwantiragin shekara ɗaya bayan ya bar Aston Villa a bazara. Ɗan wasan, mai shekaru 38, ya zama ɗan wasa na farko da Everton ta saya a ƙarƙashin kocinta Sean Dyche kuma har ya riga ya haɗe da sauran 'yan wasan ƙungiyar a sansanin da suke shirin tunkarar kakar wasa ta bana a ƙasar Switzerland. An fahimci cewa Young ya fara tattaunawa da Luton kuma waɗansu ƙungiyoyi a Saudiyya sun nuna sha'awarsu, amma daga baya ya yanke shawarar komawa Everton. Mai tsaron bayan ya lashe gasar Europa da League…
Read More
‘Yan wasan Kano Pillars sun fara hutun mako guda bayan nasarar dawowa NPFL

‘Yan wasan Kano Pillars sun fara hutun mako guda bayan nasarar dawowa NPFL

Daga BASHIR ISAH Hukumar kula da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars ta bai wa 'yan wasan ƙungiyar hutun mako guda bayan da ƙungiyar ta samu nasarar zuwa Gasar Firimiyar Nijeriya. Hakan na ƙunshe ne cikin sanarwar da shugaban ƙungiyar, Babangida Umar, ya fitar jim kaɗan bayan kammala wasan ƙarshe na ƙungiyoyi takwas da ake kira da 'super 8' na Gasar Firimiyar Nijeriya wanda ya gudana a filin wasa na Stephen Keshi da ke Asaba, Jihar Delta. Umar ya ce shugabannin ƙungiyar ba za su tafi hutu ba har sai sun miƙa rahotonsu na wannan kaka. Shuganan kulob ɗin ya…
Read More
Ancelotti zai koma horar da ’yan wasan Brazil

Ancelotti zai koma horar da ’yan wasan Brazil

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Kocin Real Madrid, Carlo Ancelotti zai karɓi ragamar horar da Tawagar Ƙwallon Ƙafar Brazil a kaka mai zuwa kamar yadda shugaban hukumar ƙwallon ƙafar ƙasar, Ednaldo Rodrigues ya bayyana. Brazil wadda ta lashe kofin duniya har sau biyar, na da kwarin guiwar cewa, Ancelotti, shi ne zai jagoranci ƙasar zuwa gasar Copa America da za ta gudana a cikin watan Yunin 2024. Brazil ba ta da wani tsayayyen koci tun lokacin da aka kammala gasar kofin duniya a bara, bayan da kocinta Tite ya yi murabus jim kaɗan da aka lallasa a hannun Croatia. Ancelotti zai…
Read More
Asamoa Gyan ya yi ritaya daga ƙwallon ƙafa

Asamoa Gyan ya yi ritaya daga ƙwallon ƙafa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Shahararren ɗan wasan ƙwallon ƙafar ƙasar Ghana, Asamoah Gyan ya sanar da yin murabus daga buga ƙwallon ƙafa. A wata sanarwa, Gyan ya ce lokaci ya yi da zai ajiye aikin taka leda a cikin mutunci. Ɗan wasan ya ci kwallaye 51 daga wasanni 109 daya buga wa ƙasarsa, lamarin da ya sa ya zama ɗan wasan Ghana a ya fi cin ƙwallaye a tawagar ƙwallon ƙafar ƙasar. Ɗan wasan mai shekaru 37 ya fara sana’ar ƙwallon ƙafa ce a shekarar 2003 tare da ƙungiyar ƙwallon Liberty Professionals, inda daga bisani ya koma Turai, ya fara…
Read More
Ronaldo ya kafa sabon tarihi a duniyar ƙwallon ƙafa

Ronaldo ya kafa sabon tarihi a duniyar ƙwallon ƙafa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Kyaftin ɗin Portugal Cristiano Ronaldo ya kafa sabon tarihin zama ɗan wasa na farko da ya buga wasannin ƙasa da ƙasa 200 a wasan neman gurbin shiga gasar kofin nahiyar Turai ta Euro 2024 da suka doke Iceland da ci 1-0. Ɗan wasan mai shekaru 38 shine ya ci ƙwallon da ta bai wa Purtgal nasara a mintuna na 89 ana daf da ƙarƙare wasa. Da farko alƙali ya zaci ƙwallon satar fage ce, amma na’urar VAR ya amince da cin lamarin da ya faranta wa Ronaldo a daren mai cike da tarihi. Wannan ita ce…
Read More
Gwamnatin Kano ta amince da naɗin kwamitin riƙo na ƙungiyar Kano Pillars

Gwamnatin Kano ta amince da naɗin kwamitin riƙo na ƙungiyar Kano Pillars

Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano Gwamnan Jihar Kano Engr. Abba Kabir Yusuf, ya amince da naɗin kwamitin riƙo na ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars (Sai Masu Gida). A cewar sanarwar da Babban Sakataren Yaɗa Labaran Gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya sanyawa hannu, ta ce, gwamnati ta naɗa shugaban hukumar da mambobi da sakatare da suka haɗa da: Babangida Little, Shugaba Garba Umar, Member Naziru Aminu Abubakar, memba Bashir Chilla, memba Ali Nayara Mai Samba, memba Shuaibu Ibrahim Doguwa, memba Rabiu Pele, memba Muhammed Danjuma, memba Sabo Chokalinka, memba Abba Haruna (Dala FM), mamba Engr. Usman Kofar Na’isa Yakubu…
Read More
Ba zan zauna a PSG har ƙarshen 2024 ba – Mbappe

Ba zan zauna a PSG har ƙarshen 2024 ba – Mbappe

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Kylian Mbappe ya ce, ya sanar da ƙungiyar Paris St-Germain a cikin watan Yulin 2022 cewar ba zai zauna a ƙungiyar fiye da ƙarshen kakar 2024 ba. Yarjejeniyar ɗan wasan mai shekara 24 za ta ƙare a ƙarshen baɗi da cewar za a iya tsawaita masa shekara ɗaya. A baya ya aika wa ƙungiyar da wasiƙar cewar ba zai cigaba da buga wasa a ƙungiyar da zarar wa'adinsa ya cika a birnin Faris. Kenan PSG za ta yi shirin sayar da Mbappe a kakar nan, idan ba haka ba za ta yi asararsa a matakin wanda…
Read More
AFCON 2024: Tawaga takwas sun sami gurbin shiga gasar

AFCON 2024: Tawaga takwas sun sami gurbin shiga gasar

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Tawagar Ƙwallon Ƙafa takwas sun sami gurbin buga gasar kofin nahiyar Afirka da Ivory Coast za ta karvi baƙunci a 2024. Masar ce ta takwas da ta samu gurbin tawaga 24 da za su kece raini a baɗi, bayan da ta ci Guinea 2-1 ranar Laraba. Kenan Masar za ta kafa tarihin shiga gasar karo na 26, ba wadda ta kai ƙasar yawan buga wasanni a gasar. Masar ce ta ja ragamar rukuni na huɗu da maki 12, kuma saura wasa ɗaya ya rage a kammala karawar cikin rukuni, inda Guinea ta ke ta biyu da…
Read More