Wasanni

Man City ta kafa tarihin lashe kofuna uku a kaka guda

Man City ta kafa tarihin lashe kofuna uku a kaka guda

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Bayan nasarar Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa ta Manchester City wajen lashe kofin zakarun Turai inda ta doke Inter Milan da ƙwallo 1 mai ban haushi, ƙungiyar ta goge guda cikin tarihin da takwararta Manchester United ke tunkaho da shi wato lashe kofunan mabanbantan gasa har guda 3 a kaka guda. Guardiola ya lashe kofin FA bayan doke Manchester United kana ya yi ƙasa da Arsenal wajen lashe Firimiyar Ingila daga bisani kuma ya je Istanbul ya doke Inter Milan a wasan ƙarshen na zakarun Turai, nasarar lashe waɗannan kofuna 3 ta ba shi damar yin kankankan da…
Read More
Za a sanar da jadawalin Firimiya na 2023/24 a makon gobe

Za a sanar da jadawalin Firimiya na 2023/24 a makon gobe

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Za a bayyana jadawalin Firimiya na gasar 2023/23 a ranar Alhamis, 15 ga watan Yunin 2023. Lokacin ne za a fayyace ranakun da za a buga dukkan karawa 380 da lokutan da za a yi wasannin. Za a fara kakar Firimiya ta 2023/24 ranar Asabar 12 ga watan Agustan 2023 - za kuma a yi wasannin ƙarshe ranar Lahadi 19 ga watan Mayun 2024. Wannan ce kakar farko da za a fara ba tare da cin karo da tsaiko ba, bayan da cutar Korona ta haifar da koma-baya na kaka biyu. Sannan a kakar nan gasar…
Read More
Benzema ya koma Al-Ittahad ta Saudiyya

Benzema ya koma Al-Ittahad ta Saudiyya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Karim Benzema ya koma Al-Ittihad kan yarjejeniyar kaka uku, in ji wata majiya daga ƙungiyar ta Jeddah, wadda ta sanar da kamfanin dillacin labarai na AFP. Ranar Lahadi Real Madrid ta sanar cewar tsohon ɗan wasan Faransa mai shekara 35 zai bar Santiago Bernabeu, bayan shekara 14 da ya yi a Sifaniya. Idan har ta tabbata cewa Benzema ya koma Saudiyya, to zai taka leda tare da tsohon ɗan ƙwallon Real Madrid, Cristiano Ronaldo mai wasa a ƙungiyar Al Nassr. Ronaldo ya koma Saudiyya da taka leda daga Manchester United a watan Janairun 2023, bayan da…
Read More
Gasar U20: Nijeriya ta lallasa Argentina a wasan daf da ƙarshe

Gasar U20: Nijeriya ta lallasa Argentina a wasan daf da ƙarshe

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Nijeriya ta bai wa Argentina mamaki inda ta doke ta da ci 2-0 sannan ta samu damar shiga gasar kofin duniya ta ’yan ƙasa da shekaru 20 a matakin daf da na kusa da ƙarshe, sakamakon ƙwallayen da Ibrahim Muhammad da Rilwanu Haliru Sarki suka ci bayan rabin lokaci. Flying Eagles sun fara haskakawa, amma yayin da aka fara wasan farko a La Albiceleste sun ɗan yi sanyi. Veliz ya zura ƙwallo biyu a raga yayin da ake daf da tafiya hutun rabin lokaci, inda ya doki ɗaya da kyar sannan ya zura ɗayan a hannun…
Read More
Sevilla ta lashe kofin Europa bayan doke Roma

Sevilla ta lashe kofin Europa bayan doke Roma

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Sevilla ta doke Roma a bugun fenariti tare da lashe kofin Europa karo na 7 yayin wasansa ƙarshe cikin daren Laraba a filin wasa na Puskas Arena da ke Budapest. Tun farko Dybala ya fara zurawa Roma ƙwallonta a minti na 34 da taimakon Mancini amma bayan dawowa daga hutun rabin lokaci Sevilla ta farke sakamakon kuskuren zura ƙwallon da Mancini ya yi a ragarsu, dalilin da ya sa kenan har aka kai ƙarshen wasa ana ƙwallo 1-1. Bayan ƙarƙare hatta ƙarin lokacin da aka yi wa karawar ta jiya ne kuma aka tafi bugun fenariti…
Read More
Hada-hadar kasuwar ’yan wasan ƙwallon ƙafa

Hada-hadar kasuwar ’yan wasan ƙwallon ƙafa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ɗan wasan gaba a Portugal Cristiano Ronaldo na son barin ƙungiyar Al Nassr ta Saudiyya, babu mamakin ya dawo Turai. Juventus ta jadadda cewa ɗan wasanta, Dusan Vlahovic mai shekara 23 daga Serbia ba na sayarwa ba ne, ta fitar da wannan sanarwa ne ganin rububin da aka soma a kansa. Ƙungiyar Fenerbahce ta Turkiyya na kan gaba a cinikin saye ɗan wasan Belgium da Ac Milan Divock Origi, wanda ke cika shekara guda da barinsa Liverpool. Tottenham na duba yiwuwar tuntuɓar kocin Feyenoord, Arne Slot. Slot na iya zama sabon kocin Tottenham idan aka daidaita…
Read More
Alba na shirin barin Barcelona kafin ƙarewar kwantaraginsa

Alba na shirin barin Barcelona kafin ƙarewar kwantaraginsa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Barcelona da Jordi Alba sun cimma yarjejeniyar raba gari tun kan kwantiraginsa ya ƙare a ƙungiyar. Alba, mai shekara 34 ya koma Camp Nou a 2012 daga Valencia, ya kuma lashe La Liga shida da Copa del Rey biyar da gasar Zakarun Turai a 2015. Ya buga wa Barcelona wasanni 458 har da 29 a kakar nan da ƙungiyar Camp Nou ta ɗauki La Liga na bana na 27 jimilla. Alba ya zama na biyu da zai bar Barcelona a aarshen kakar nan, bayan kyaftin, Sergio Busquets. Barcelona ta kai ga cimma wannan matsaya, bayan da…
Read More
Newcastle za ta shiga gasar Zakarun Turai karon farko cikin shekaru 20

Newcastle za ta shiga gasar Zakarun Turai karon farko cikin shekaru 20

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa ta Newcastle ta samu damar kaiwa matakin iya taka leda a gasar kofin Zakarun Turai karon farko cikin shekaru 20, kasa da kakar wasa biyu bayan ƙungiyar ta kwaci kanta da kyar daga rukunin ’yan daga aji na teburin firimiya, wanda ya kai ga sayar da ita. Newcastle United dai na shirin kammala kakar ta bana a matsayin ta 3 a teburin firimiyar Ingila bayan da ta yi canjaras da Leicester City a jiya Litinin wanda ke nuna yanzu ta na da maki 70 ne bayan doka wasanni 37 tazarar maki 1 tsakaninta…
Read More
Hada-hadar kasuwar ’yan wasan ƙwallon ƙafa

Hada-hadar kasuwar ’yan wasan ƙwallon ƙafa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ɗan wasan tsakiya na Arsenal da Norway Martin Odegaard na shirin ƙulla sabuwar yarjejeniya da ƙungiyar kasancewar kwantiraginsa na yanzu zai kare a 2025. Kocin Bayer Leverkusen Xabi Alonso ya bayar da tabbacin ci gaba da zama a ƙungiyar ta Jamus a kaka ta gaba bayan da aka riƙa danganta tsohon ɗan wasan na Liverpool da aikin kocin Tottenham da ba kowa a yanzu. Ɗan wasan Arsenal Albert Sambi Lokonga, mai shekara 23, zai so tafiya Burnley domin sake haɗewa da kociya Vincent Kompany, wanda ya koyar da ɗan Belgium ɗin a Anderlecht. Ɗan wasan Ivory…
Read More
Xherdan Shaqiri ya zama ɗan wasa mafi yawan albashi a MLS ta Amurka

Xherdan Shaqiri ya zama ɗan wasa mafi yawan albashi a MLS ta Amurka

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Wasu bayanai na nuna cewa ɗan wasan gaba na Switzerland Xherdan Shaqiri shi ne ɗan wasa mafi ɗaukar albashi a Lig ɗin MLS da ke Amurka. Bayanan da aka fitar a ranar Talata sun nuna cewa, Shaqiri da ke taka leda da Chicago Fire na ɗaukar albashin dala miliyan 8 da rabi yayin da Lorenzo Insigne da ke taka leda da Toronto ke ɗaukar albashin dala miliyan 7 da rabi kana Javier Hernandez na Los Angeles Galaxy a matsayin na 3 da albashin dala miliyan 7. Shaqiri mai shekaru 31 wanda ya taka leda da ƙungiyoyin…
Read More