Wasanni

Hoto: Gwamna Bala ya yi maraba da Gamal

Hoto: Gwamna Bala ya yi maraba da Gamal

A kwannan ne ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta jihar Bauchi, Wikki Tourist, ta samu sabon ɗan wasa daga ƙasar Masar, Mahmud Gamal, inda zai ci gaba da ɓarje gyaɗarsa a fagen ta-maula a ƙungiyar. Da wannan ne Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya yi wa sabon ɗan wasan marhabin da zuwa Bauchi, tare kuma da miƙa masa kayayyakin da zai riƙa amfani da su wajen buga wasanni.
Read More
Perez ya zama shugaban Real Madrid karo na 6

Perez ya zama shugaban Real Madrid karo na 6

Daga BASHIR ISAH An sake zaɓen Florentino Perez ba tare da hamayya ba a matsayin shugaban ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid a karo na shida. Perez mai shekara 74, shi ne kaɗai ya kasance wanda ya tsaya takarar neman matsayin tun bayan da aka buɗe ƙofar takara. Ko a 2013 da 2017 Perez ya taki wannan matsayi bayan da ya yi takarar ba tare da wata hamayya ba. A matsayinsa na zaɓaɓɓen shugaban ƙungiyar, ana sa ran dattijon ya ja ragamar ƙungiyar ya zuwa 2025.
Read More
Ahmed Musa ya shirya komawa Kano Pillars – Rahoto

Ahmed Musa ya shirya komawa Kano Pillars – Rahoto

Daga WAKILINMU Rahotanni sun tabbatar cewa fitaccen ɗan wasan ƙwallon ƙafar nan kuma kyaftin a Super Eagles, wato Ahmed Musa, na shirin sake komawa ƙungiyar Kano Pillars don yin aiki na taƙaitaccen lokaci. Musa, ɗan shekara 28, ya kasance ba ya buga ma wata kulob wasa tun daga Otoban 2020, bayan kammala harƙallarsa da ƙungiyar Al Nassr ta ƙasar Saudiyya, bayan kuma ya kasa samu ƙulla wata harka a Turai. Bayanai sun nuna ana sa ran tsohon ɗan wasan Leicester City ɗin zai yi aiki na ɗan lokaci tare da Kano Pillars. Kanawa na matuƙar martaba ɗan wasan tun bayan…
Read More
Wasanni: Dare ya gargaɗi ‘yan wasa su guji yin amfani da muggan ƙwayoyi

Wasanni: Dare ya gargaɗi ‘yan wasa su guji yin amfani da muggan ƙwayoyi

Daga BASHIR ISAH Ministan Wasannin Motsa Jiki, Chief Sunday Dare, ya yi kira ga 'yan wasa da su guji yin amfani da ƙwayoyin ƙara kuzari da duk wani nau'i na fitina. Ministan ya yi wannan kira ne yayin rangadin da ya je don duba wuraren wasanni na bikin wasannin motsa jiki na ƙasa (NSF) karo na 20 da ke gudana a Benin, babban birnin jihar Edo. Dare wanda shi ne ya wakilci Mataimakin Shugaban Ƙasa, Yemi Osinbajo a wajen taron buɗe bikin, ya ce bikin zai taimaka wajen gano 'yan ƙasa masu fasaha a sha'anin wasannin motsa jiki. Binciken Manhaja…
Read More
Koriya ta Arewa ta janye daga gasar Olympics saboda tsoron cutar korona

Koriya ta Arewa ta janye daga gasar Olympics saboda tsoron cutar korona

Daga WAKILINMU Koriya ta Arewa ta bada sanarwar ba za ta halarci gasar Olympics da aka shirya gudanarwa a Ƙasar Tokyo ba a cikin wannan shekara saboda dalili na neman kare 'yan wasanta daga kamuwa da cutar korona. Koriya ta Arewa ta ce na musamman ta ɗauki wannan mataki domin kare 'yan wasanta gudun kada su harbu da cutar korona. Wannan mataki da ƙasar ta ɗauka ya katse wa Koriya ta Kudu damar da ta hango na yin amfani da gasar wajen tattaunawa da takwararta Koriya ta Arewa game da abin da ya shafi kan iyaka. A 2018 ƙasashen biyu…
Read More
Ondo: ‘Yanwasan Sunshine Stars sun yi zanga-zanga saboda rashin biyan albashi

Ondo: ‘Yanwasan Sunshine Stars sun yi zanga-zanga saboda rashin biyan albashi

Daga UMAR M. GOMBE 'Yanwasa da jami'an Ƙungiyar Ƙwallon Kafa ta Sunshine Stars a Jihar Ondo, sun gudanar da zanga-zanga domin nuna rashin jin daɗinsu kan abin da suka kira da rashin kulawa daga ɓangaren Gwamnatin Jihar. Zanga-zangar wadda aka gudanar a birnin Akure ta yi sanadiyar haifar da tsaiko ga harkokin kasuwanci a yankin. Masu zanga-zangar sun yi tattaki ne daga babban filin wasannin motsa jiki zuwa fadar gwamnatin jihar ɗauke da kwalaye masu dauke da saƙonni daban-daban don nuna damuwarsu. Waɗanda lamarin ya shafa sun ce ba su samu albashinsu ba na tsawon wata shida haɗa da sauran…
Read More
AFCON 2022: Super Eagles ta tsallake siraɗi

AFCON 2022: Super Eagles ta tsallake siraɗi

Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa ta Nijeriya, Super Eagles, ta samu nasarar shiga gasar Cin Ƙofin Ƙasashen Afirka (AFCON) wadda aka shirya gudanarwa a ƙasar Kamaru a 2022. Nijeriya ta samu wannan nasarar ce sakamakon kunnen doki na rashin jefa ƙwallo a raga da Lesotho da Saliyo suka yi a rana ta biyar na buga wasan cancantar shiga gasar.
Read More
‘Yan wasa 8000 ne za su fafata a bikin wansannin motsa jiki na Edo – Minista

‘Yan wasa 8000 ne za su fafata a bikin wansannin motsa jiki na Edo – Minista

Daga UMAR M. GOMBE Gwamnatin Tarayya ta bada tabbaccin za a gudanar da bikin wasannin motsa jiki da aka shirya gudanarwa a jihar Edo kamar yadda aka tsara. Ministan Harkokin Matasa da Wasannin Motsa Jiki, Chief Sunday Dare ne ya bada wannan tabbaci a garin Benin, Juma'ar da ta gabata. A cewar Dare, bikin wanda ake sa ran ya ƙunshi 'yan wasa 8000, zai gudana ne daga ranar 2 zuwa 4 ga Afrilun 2021. Da yake jawabi bayan kammala zagayen duba kayayyakin wasa da kuma ganawa da gwamnan jihar, Godwin Obaseki, Ministan ya ce, "za a buɗe sansanin 'yan wasa…
Read More
Kenya: An yanke wa ‘yar wasan tsere hukuncin shekara guda saboda amfani da maganin ƙara kuzari

Kenya: An yanke wa ‘yar wasan tsere hukuncin shekara guda saboda amfani da maganin ƙara kuzari

Daga FATUHU MUSTAPHA Wata kotun ƙasar Kenya ta yanke wa ‘yar wasan tseren asar, Florence Jepkosgei, hukuncin yi wa al’umma hidima na tsawon shekara guda bayan da ta kama ta da laifin gabatar da takardun bogi na ƙoƙarin kare kanta daga laifin yin amfani da ƙwayoyin ƙara kuzari, in ji Ƙungiyar Yaƙi da Amfani da Abubuwan Ƙara Kuazara ga ‘Yanwasa ta Kenya (ADAK). Da wannan, Florence ta zama ‘yar tseren Kenya ta farko da aka taɓa yanke wa hukuncin manyan laifuka a kotu. An shafe shekaru ana gudanar da bincike kan wannan batu kafin a kai ga yanke hukunci a…
Read More