22
Jul
Daga UMAR M. GOMBE Kwamitin Shirya Wasannin Olympic na Ƙasa da Ƙasa ya bayyana birnin Brisbane na ƙasar Australia a matsayin birnin da zai ɗauki nauyin gudanar da Wasannin Olympic na 2032. Da wannan sasarar da Brisbane ya samu, ya sanya Australia ta zama ƙasa ta biyu a duniya bayan ƙasar Amurka da suka samu damar ɗaukar nauyin gudanar da Wasannin Olympic fiye da sau biyu a birane daban-daban. Da farko, Australia ta soma ɗaukar nauyin Olympic ne a Melbourne a 1956, sannan Sydney a 2000, sai kuma na ukun kenan ake sa ran gudanarwa a Brisbane ya zuwa 2032.…
