27
Jan
Hukumar Kwallon Kafa ta Nahiyar Turai (UEFA), ta fitar da jerin ’yan wasan da masoya kwallon kafa suka zaba mata, a matsayin tawagar fitattun ’yan wasan ta na shekarar 2020. UEFA ta bai wa masoya kwallon kafa damar soma kada kuri’un su wajen zaba ma ta tawagar ’yan wasa 11 daga ranar 30 ga watan Nuwamba zuwa 6 ga Janairun da muke ciki, inda ’yan wasan Bayern Munich suka fi na kowace kungiya yawa. Tawagar ta shekarar 2020 ko kakar wasan da ta kare, ta kunshi Manuel Neuer na Bayern Munich a matsayin mai tsaron raga. Masu tsaron baya kuma…
