Ƙungiyar Likitoci ta Ƙasa (NARD), za ta fara yajin aikin gargaɗi na kwana biyar.
Ƙungiyar ta ce ta ɗauki wannan mataki ne bayan da Gwamnatin Tarayya ta gaza wajen cimma buƙatun mambobinta.
Sanarwar da ƙungiyar ta fitar ranar Litinin ta ce, an cimma shawarar fara yajin aikin ne bayan taron da shugabanin ƙungiyar suka gudanar ta bidiyo inda suka shafe sa’o’i shida da rabi suna tattaunawa
Likitocin sun ce yajin aikin zai fara ne daga ƙarfe 8:00 na safiyar ranar Larba, 17 ga Mayu, sannan ya ƙare ran Litinin, 22 ga Mayu da ƙarfe 8:00 na safe.
Kafin wannan lokaci NARD ta ƙayyade wa gwamnati wa’adin makonni a kan ta cika mata buƙatunta ko kuma ta tafi yajin aiki.
Wa’adin da ya riga da ya cika a ranar Asabar 13 ga Mayu, 2023.