Dapo Abiodun ya lashe zaɓen Gwamnan Jihar Ogun

Daga SANI AHMAD GIWA

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), ta bayyana Dapo Abiodun na Jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen Gwamnan Jihar Ogun da aka gudanar ranar Asabar.

Jami’in zaɓen, Farfesa Kayode Adebowale ne ya sanar da shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen bayan kammala tattara sakamakon zaɓen ƙananan hukumomi 20 na jihar.

Abiodun ya samu ƙuri’u 276,298 inda ya doke Ladi Adebutu na Jam’iyyar PDP mai ƙuri’u 262,383.

Biyi Otegbeye na Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ya zo na uku.