El-Rufa’i ya shigar da Majalisar Dokokin Kaduna ƙara kan badaƙalar Naira biliyan 432

Daga BALA MUHAMMAD

Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa’i, ya shigar da Majalisar Dokokin Jihar ƙara kan kuɗi da adadinsu ya kai naira biliyan 432 da suka zargi gwamnatinsa da sauya akalansu.

El-Rufa’i ya shigar da ƙarar takardar nuna ƴancinsa da ke ƙalubalantar zargin shi da cin hanci da kwamitin Majalisar ta yi a babbar kotun tarayya da ke Kaduna.

Lauyansa Abdulhakeem Mustafa (SAN) shi ya jagoranci shigar da ƙarar inda a ciki El-Rufa’i ya buƙaci kotun da ta yi watsi da rahoton kwamitin majalisar da ke tuhumarsa da gwamnatinsa da cin hanci, ganin cewa ba a bashi damar jin ta bakinsa ba.

A farkon watannan ne majalisar ta naɗa kwamitin domin bincike kan lumuran da suka shafi kuɗaɗe da aka ware na ayyuka da na aro a gwamnatin El-Rufa’i.

Shugaban kwamitin, Henry Zacharia, ya ce mafi yawancin kuɗaɗen aron ba a yi amfani da su ba kan abin da aka karɓo su a kai, sannan kuma a wani ɓangare ba a cike ƙa’idoji wajen karɓowa ba.

Kakakin Majalisar, Yusuf Liman ya ce, a kalla kuɗaɗen za su kai kimanin naira biliyan 432 inda suka buƙaci a binciki El-Rufa’i da muƙarrabansa kan cin mutuncin aiki da sauya akalan dukiyar al’umma gami da satar kuɗi, sannan kuma a gaggauta dakatar da kwamishinar kuɗi, Shizer Badda wacce ita ma mai muƙami ce a gwamnatinnasa.

Leave a Reply