Farashin gangar mai ya kai Dala 110 dalilin yaƙin Rasha da Ukraine

Farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya ya tashi zuwa Dala 110 kowacce ganga, sakamakon fargabar da ake da ita na yaƙin da ke gudana a Ukraine da kuma takunkumin karya tattalin arzikin da ƙasashen duniya ke ƙaƙaba wa Rasha.

Rahotanni sun ce masu zuba jari da masu masana’antu na fargabar katsewar samun man a daidai lokacin da suke ƙoƙarin farfaɗo wa daga annobar Korona, wadda ta yi wa ƙasashen duniya illa.

Yau ake sa ran ƙungiyar ƙasashe masu arzikin man fetur ta OPEC, ta gudanar da taro domin duba yadda za a ƙara yawan man da ake kaiwa kasuwannin duniya domin daidaita farashinsa.

Irin wannan yunƙuri a watan jiya bai haifar da ɗa mai ido ba, ganin yadda ƙasashen suka kasa cimma yarjejeniya a tsakaninsu na qara yawan man da suke haƙowa kowacce rana.

Ƙasar Rasha da ke fuskantar takunkumin karya tattalin arziki, na ɗaya daga cikin manyan ƙasashen da suka fi fitar da man zuwa kasuwannin duniya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *