Daga AMINA YUSUF ALI
Gobara ta lamushe wata kasuwa da ake kira Gamboru a cikin birnin Maiduguri, babban birnin jihar Borno.
Kasuwar Gamboru ita ce kasuwar sayar da kayan gwari mafi girma a garin Maiduguri.
Ya zuwa haɗa wannan labari ba a san musabbabin gobarar ba, amma majiyarmu ta bayyana cewa, an rasa dukiya ta ɗaruruwan miliyoyin Nairori.
Gobarar ta afku ne bayan ɓarkewar wata gobarar daban a sassafiyar Asabar ɗin a kasuwar Biu da ke a Kudancin jihar Borno.