Guinea: ECOWAS ta buƙaci a gaggauta sako Conde, maido da gwamnatin ƙasar kan tsarin da aka san ta

Ƙungiyar Bunƙasa Tattalin Arzikin Ƙasashen Yammacin Afirka ECOWAS ta buƙaci sojojin Tarayyar Guinea da ke riƙe da Shugaban Ƙasar, Alpha Conde, da su gaggauta sako shugaban haɗa da dukkan jami’an da suke riƙe da su ba tare da gindaya wani sharaɗi ba.

Cikin wata sanarwar bayan taro da ta fitar a ranar Lahadi wadda ta sami sa hannun Shugaban Ƙasar Ghana, Nana Addo Dankwa Akufo-Addo, ECOWAS ta nuna takaicinta tare da yin Allah-wadai da wannan mummunan al’amari da sojojin Guinea suka aikata na yunƙurin kifar da gwamnatin Conde.

ECOWAS ta kuma buƙaci ba tare da ɓata lokaci ba, a gaggauta maida gwamnatin ƙasar bisa tsarinta na dimukuraɗiyya kamar yadda aka santa.

Kana ta yi kira ga jami’an tsaron da ke bada kariya da su yi tsayin daka wajen ci gaba da aikinsu.

Daga nan, ECOWAS ta nuna goyon bayanta ga gwamnatin Guinea da al’ummarta na ci gaba da zama ƙasa mai tsarin mulkin dimukuraɗiyya.

A Lahadin da ta gabata sojojin ƙasar Guinea ƙarƙashin jagorancin Kanal Mamadi Doumbouya suka yi iƙirarin kifar da gwamnatin ƙasar da kuma kama Shugaba Conde tare da wasu manyan jami’an gwamnatinsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *