Gwamnatin Tarayya ta haƙiƙance kan biyan naira dubu 62 mafi ƙarancin albashi ga ma’aikata

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Gwamnatin Tarayya ta ce naira dubu 250 da hukumar ƙwadago suka buƙaci ta ke biya a matsayin mafi ƙarancin albashi ga ma’aikata abu ne mai nauyi a gareta inda take ganin adadin ya yi yawan da ba zata iya kikayewa ba.

Gwamnatin ta yi sanarwar ne ta ofishin mai taimakawa Shugaba Tinubu kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga a ranar Lahadi biyo bayan nuna damuwa da ƙungiyar ƙananan hukumomin Najeriya ta yi kan naira dubu 62 da gwamnatin ta sanar zata ke biya a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi ga ma’aikatan ƙasar.

A ranar 28 ga watan Mayu, 2024 ne aka yi zama tsakanin gwamnatin tarayya da ƙungiyar ƙwadago ta NLC, kan dubu 62 wanda gwamnatin tare da ƙungiyar haɗaɗɗun kamfanoni suka amince za su iya biya inda wakilan ƙungiyar suka ƙi amincewa da hakan.

Ƙungiyoyin ƙwadon sun bayyana buƙatar gwamnati na biyan dubu 62 a matsayin zagi da cin mutuncin tsaka-tsakin ma’aikaci inda ta ce ya cancanci sama da abun da gwamnatin ke ƙudurin biya.

Onanuga ya bayyanawa manema labarai cewa, matuƙar gwamnati ta amince biyan yadda ƙungiyar ƙwadago ke buƙata, to za’a talauta asusun ƙuɗin ƙasa inda ya ce amsawa hakan, son kai ne, domin bada wannan kaso ga ƴan ƙasa da basu fi kashi 10 cikin 100 ba na ƴan Najeriya, rashin adalci ne ga dukiyar ƙasa.

Sannan ya ƙara da cewa, akwai buƙatar NLC ta sake nazari kan hukuncinta, saboda akwai ayyuka da dama da gwamnatin tarayya ke yi. Haka kuma, sun tattauna da wakilan ƙungiyar haɗaɗɗun kamfanoni wanda shima abun la’akari ne, dan haka suke kira ga ƙungiyar cewa ta sake shawara.

Daga ƙarshe, ya ce suna jira su ji sabon jawabin ƙungiyar daga yanzu zuwa bayan kammala ayyukan taron ƙungiyoyin ƙwado na duniya da ya gudana a ƙasar Switzerland.