Haɗin kan Neja da Kaduna abin yabo ne – El-Rufai

Daga BASHIR ISAH

Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya yaba wa takwaransa na jihar Neja, Abubakar Sani Bello, bisa haɗa kai da Kaduna wajen yaƙi da harkokin masu sace-sacen mutane a iyakokin Kaduna da Neja.

El-Rufai ya yi wannan yabo ne yayin ziyarar da ya kai wa Gwamna Bello a Minna, babban birnin jihar.

Babbar Sakatariyar Yaɗa Labarai ta gwamnan Neja, Mary Noel-Berje ta ce, El-Rufai ya yi ziyarar ne domin jajanta wa gwamnati da ma al’ummar jihar game da rashin wani fitaccen ɗan jihar da ya auku ba da daɗewa ba.

Yayin ziyar, Gwamana El-Rufai ya ce, Neja da Kaduna suna aiki tare wajen yaƙi da harkokin ɓatagari da suka addabe su.

Inda ya ce, “Yaƙi da waɗannan ɓatagarin shi ne babban ƙalubalen da muke fuskanta. Amma ina so in yaba wa Gwamna Sani Bello da tawagarsa dangane da yadda ake aiki tare da Kaduna. Ina kyautata zaton cewa da a ce akwai irin wannan haɗin kan da sauran jihohi, wataƙila da abubuwa sun yi kyau.”

Ya ci gaba da cewa, yana da yaƙinin nan gaba harkokin sace-sacen mutane da sauran manyan laifuka za su kau, duba da ƙoƙarin jami’an tsaro a jihohin biyu.

El-Rufai ya yi amfani da wannan dama wajen shawartar sabbin manyan hafsoshin tsaro da aka naɗa kwnan nan, da su duba su ɗora daga inda magabatansu suka tsaya wajen yaƙi da matsalolin tsaron ƙasar nan.

A nasa ɓangaren, Gwamna Abubakar Sani Bello ya jaddada cewa, gwamnati ba za ta yi ƙasa a guiwa ba har sai ta ga ƙarshen harkokin sace-sacen mutane da makamantansu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *