Hajjin 2021: Sarki Aminu ya gargaɗi maniyyatan Kano

Daga UMAR. M. GOMBE

Mai Marta Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya gargaɗi maniyyatan jihar Kano na Hajjin 2021 kan su kiyaye ban da karya dokoki ciki har da dokokin yaƙi da cutar korona da na tafiya ƙasa da ƙasa yayin da suka isa ƙasa mai tsarki, Saudiyya.

Basaraken ya ƙarfafa kan buƙatar maniyyatn su zamo masu biyayya ga dokin yaƙi da korona kana su rungumi ɗabi’ar tsafta yayin da suka shiga aikin Hajji a Daular Saudiyya.

Sarkin ya yi wannan gargaɗi ne yayin da yake buɗe taron bita kan aikin Hajji na 2021 a Kano.

Taron wayar da kan, taro ne wanda aka saba gudanarwa don faɗakar da maniyyat game da ayyukan Hajji kamar yadda addinin Musulunci ya tsara a gudanar a ƙasa mai tsarki.

Hukumar Alhazai ta Jihar Kano ita ce ta shirya wannan taron bitar yayin da ya rage wasu ‘yan watanni kafin a soma jigilar alhazai daga Kano zuwa Saudiyya.

Sarki Aminu ya yi tunatarwa kan cewa wannan karo za a samu sauƙin jigilar maniyyata da kuma gudanar da sauran ayyukan Hajjin bana sakamakon annobar korona wadda ta yi sanadiyar samun saye-sauye da dama.

Haka nan, ya ce kamar sauran maniyyata daga sassan duniya su ma maniyyatan Nijeriya ana bukatar su zama masu bin dokoki sau da ƙafa, tare da cewa ba ya so ya ji an samu wani maniyyacin Kano da aikata wani laifi.

Ta bakin Basaraken, ”Yanayin aikin Hajji ya sauya daga abin da kowa ya sani a baya, ya zama wajibi ku zauna da shirin karɓar sabbin tsare-tsare. Annobar korona ita ce abar da ta haifar da canje-canje ga komai a duniya.

“Don haka an buɗe wannan taro, kuma ana sa ran maniyyata su koyi yadda za a aiwatar da sabbin tsare-tsaren da aka samu. Za ku fuskanci sabon tsari da kuma ƙa’idoji. Kada ku bari a bar ku a baya.”

A nasa ɓangaren, Gwamnan Kano, Abdullah Umar Ganduje, ya yi jan hankali ga maniyyatan Kano da su zama jakadun Kano nagartattu yayin zamansu a Saudiyya.

Gwamnan ya bayyana hakan ne ta bakin wakilinsa a wajen taron, Alhaji Usman Alhaji kuma Sakataren Gwamnatin Jihar, tare da bai wa shugabannin ƙananan hukumomi 44 da jihar ke da su umarni kan su bai wa Hukumar Alhazan Jihar cikekken haɗin kan da take buƙata daga gare su.

Shi kuwa Sakataren Hukumar Alhazan Jihar, Alhaji Abba Mohammad Dambatta, cewa ya yi taron bitar zai gudana ne mako-mako a cikin watan Ramadan domin bai wa maniyyatan damar sabo da sabbin tsare-tsaren aikin Hajji da aka samar.

Dambatta ya ce a shirye hukumarsu take ta kiyaye dokokin ƙasar Saudiyya da na Hukumar Hajji ta Nijeriya (NAHCON). Kana ya yaba da irin goyon bayan da Gwamna Ganduje ke bai wa hukumarsu a kowane lokaci.