Daga TIDZALLA ZACCHAEUS a Nasarawa
Gwamnan Jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule, ya kaɗa ƙuri’arsa a mazaɓarsa mai lamba 001 da ke Gudi, cikin Ƙaramar Hukumar Akwanga.
Ya kaɗa ƙuri’ar ce da da misalin ƙarfe 11:49 tare da matansa biyu.
Gwamna Sule na daga cikin jerin gwamnonin da ke neman wa’adin mulki na biyu.



