Daga BASHIR ISAH
Bankin Duniya ya jadda aniyarsa na tallafa wa ilimin ‘ya’ya mata a Nijeriya inda ya sake ware Dala miliyan $700 a matsayin gudunmawarsa ga fannin ilimin na ‘ya’ya mata a ƙasar.
Dala miliyan $700 ɗin ƙari ne a kan abin da Bankin ya bayar a baya.
Bankin ya ce, ya ba da tallafin ne domin bai wa ‘ya’ya mata marasa galihu damar kammala karatun sakandare.
A baya Bankin ya ba da tallafin Dala miliyan $500 don tallafa wa karatun ‘ya’ya mata a wasu jihohi 7 na ƙasar.
A cewar Bankin tallafin baya-bayan zai shafi wasu jihohin ƙasar su 19 ne.
Daraktan Bankin a Nijeriya, Shubham Chaudhuri, shi ne ya yi waɗannan bayanan ranar Litinin a Abuja.