Jahilai ke ganin kuskuren shigar malamai siyasa – Sheikh Ibrahim Khalil

Daga MUHAMMADU MUJTABA USMAN a Kano

Blueprint Manhaja ta samu zarafin zantawa da Shugaban Majalisar Malamai na Arewa, Sheikh Ibrahim Khalil akan wasu muhimman alamura da suka shafi siyasa kai-tsaye, har ma da addini da kuma dalilinsa na daɗewa bai je umara ba da kuma dalilinsa na neman zama Gwamnan Jihar Kano a jamiyarsa ta ADC a kakar zaɓe mai zuwa ta 2023. Sannan kuma ya faɗi dalilin da ya sa ake ce wa mutanan kirki su shigo siyasa da gaskiyar lamarin da sauran batutuwa da wakilinmu, Muhamadu Mujitaba bin Usman, ya tattauna da shehin malamin a gidansa da ke Birnin Kano a ranar Laraba da ta gabata. A sha karatu lafiya.     

MANHAJA: Malam, ko me za ka ce a game da saukar ‘yan siyasa masu riƙe da muqamai a matakin jiha da ma na ƙasa a wannan lokaci?
KHALIL: Da sunan Ubangiji mai rahama, mai jin qai, tsira da Aminci su ƙara tabbata ga Shugabanmu, Annabi Muhammad (S.A.W). Da farko wannan ba wani baƙon abu  ba ne a siyasarmu ta Nijeriya, musamman idan kakar zaɓe ta zo irin wannan. Kuma musamman idan gwamna ko shugaban ƙasa yana zango na ƙarshe, buƙatar ‘yan siyasa na ƙaruwa na ganin kowa yana so ya yi takara kamar yadda doka ta ce, sai ya sauka. Wannan shi ne dalilin da ya sa ka ga waɗannan abubuwa sun faru a wannan lokaci, kuma kullum burin ɗan siyasa shi ne ya yi takara ko a dama da shi ta yadda burinsa zai cika na samun muƙami ko kuɗi kamar yadda burin wasu yan siyasar kenan. Hakan ya sa wasu masu zaɓen ba sa tantance wanne shugaba ko wanne wakili ya kamata a zaɓa da zai inganta rayuwarsu ta samu abubuwa muhimmai a rayuwa. Wanda har ta kai ga masu zaɓe na mantawa da wannan kawai sai dai a ba su kuɗi, daga baya kuma su riƙa wasu maganganu na tituna ko wani abu mai kama da haka. Wanda kuma ya kamata  kowa ya gyara tunaninsa don kawo cigaban al’umma da ƙasa.

Allah ya gafarta Malam, akwai masu cewa ya kamata malamai ku tantance duk wani ɗan siyasa da zai tsaya takarar neman wani muƙami . Me Malam yake  gani a kan wannan batu?
To, abun tambaya a nan shi ne, su waye za su tantance su, menene ƙarfinsu na faɗa a ji a doka, da sauransu? Eh, gaskiya ne malamai suna da tasiri suna kuma da mabiya. Al`umma sun yadda da su. Amma wani abu shi ne, kullum ana faɗar akasin hakan. Sai dai kuma cikin masu faɗar hakan, har da ‘yan siyasa. Amma su ba gaskiya ba ne nasu faɗin, wata manufa ce kawai domin babu mai qin malaman ko mutanan kirki ko ‘yan siyasa, suna faɗa ne domin a rage ganin laifinsu, su ma malaman a ringa ganin laifinsu. Su ma akwai mutanen kirkin a siyasa, amma gaskiya wasu ‘yan siyasar yaudara ce kawai. Idan sun ɗauke hankalin mutane daga ganin gazawarsu, amma da zai yiwu malamai su tantance abu ne mai kyau. Amma wannan zuma ake shafa wa malamai kawai a baki.

Malaman muna cikin watan Ramadan mai Alfarma ana ta ruguguwar zuwa ƙasa mai tsarki, Umara. Amma an ga ‘yan shekaru da dama Malam bai je Umara ba. Wanne darasi ne Malam yake so jama’a su koya daga malamai irinku da sauransu?
Eh, gaskiya da muna zuwa Umara kansancewar Umara abu ne mai ladan gaske. To kuma sai muka ga daga baya kamar abun ya zama gasa. Duk da yake  har yanzu wasu na zuwa ne don neman lada, amma wasu ba a san ma abunda za a kira abun ba. Kuma akwai masu ganin cewa kamar sai ka je umara ne idan ka yi Addua ko idan ka roƙi Allah zai karɓa, ba haka ba ne. Allah ya jiƙan wani malaminmu yana cewa, Addua Allah yana karɓar ta idan bawa ya yi a ko’ina ne, ko da kuwa a ɗakin RATUƘA NE. Karuwar farko a tarihin duniya tun da Allah ya karɓi Addu`arta kuma har ta sheɗan ma an karɓa. To kuma yanzu ka ga akwai buƙatu wanda za ka samu lada mai yawa ko da taimakon raunana ne da taimakon marasa lafiya a wannan lokaci, amma dai ba cewa na yi Umara ba kyau ba.

Wacce shawara ce Mallam yake da ita ga masu zave a 2023?
Shawarata shi ne, ma’auni na farko nagarta ga duk wanda za su zaɓa, musamman wanda ake da kyakkyawan zato a kansa, ko aka gwada, aka gani. A lura da wannan kuma, sannan a yi tunani cewa tunda ga 1999 zuwa 2022 wacce matsala ‘yan siyasar nan suka warware,  wacce ce kuma take damun mutane a rayuwarsu ta yau kuma su waye za su iya warware ta da taimakon Allah? To wannan abun lura ne, kada su yarda da mayaudaran ‘yan siyasa. Akwai kuma buƙatar wayewa ga masu zaɓe a kowanne mataki da za a zaɓi mutum wakili ne ko shugaba, wajibi ne mutane su fifita mai nagarta da aka san tarihinsa fiye da komai wajen zaɓan kowanne wakili ko shugaba. Wannan shi ne saƙona ga masu zaɓe a kowanne lokaci ba ma wai 2023 ba. Wajibi ne kowa ya yi hattara wajen zaɓe, kuma a banbance qiyayya da soyayya. Ma’ana, kada ka ƙi mai nagarta don ba ka ƙaunar sa, kada ka zaɓi mara kishin alumma, mara kishin ƙasa, don kana ƙaunar sa. Auna shugabannin yanzu ka ga mai suka yi wa jamaa, ko mai suka kasa yi wa jama`a. Domin jin daɗin rayuwar yau da gobe, da farin cikin da ka samu ko akasin haka, don tabbatar da abu mafi kyau a rayuwa.

A ƙarshe, Malam na ɗaya daga cikin malaman ƙasar nan, kuma malam ne shugaban majalissar malamai ta Arewacin Najeriya. Mutane da dama na da tunanin cewa matsayin malamai kamar iyaye ne na alumma, har matsayinsu ya wuce su shiga siyasa. Sai kuma ga Malam a cikin siyasa tsindum! ko me Malam zai ce a kan wannan ra'ayi na alumma?
Wato siyasa, kowa ya zama wajibi ya yi siyasa saboda larurarta saboda ‘yan siyasa ba su biya wa mutane buƙatunsu ba. don haka, ya zama dole mu a kanmu mu shiga siyasa, domin samar wa da mutane jagoranci nagari da taimakon Allah.To ai ana ganin kamar matsayin malam ya wuce siyasa, ya nemi Gwamnan kano. A’a, ba haka ba ne. Kyakkyawan misali a nan shi ne, Annabin Allah Sulaiman Alaihissalam ai sarki ne, Allah ne ya ba shi, wa yake ba da gwamna banda Allah?  Annabi Yusif Alaihissalam Annabin Allah ne kuma ai ya riqe matsayi na sarauta, da za ka iya cewa minista ne a wannan zamanin! Annabi Dauda Alaihissalam ai shugaba ne, kuma Annabin Allah ne. Kuma idan ka duba  Annabawa su ne shugabannin al`ummarsu, kuma shugabannin Annabawa da ɗaukacin halitta bakiɗaya. Annabi Muhammadu (S.A.W) ya ce, malamai su ne magada Annabawa. Babu wanda ya dace ya jagoranci al’umma kamar malami, musamman saboda dalilaina uku. Na farko, indai ka yarda malamin ne shi aka fi yi wa kyakkyawan zato na tsoron Allah. Na biyu shi ne, idan ya yi ba daidai ba, za a ce masa, kai ka ce Allah ya ce  kaza, yaya ka yi haka? Ka ga zai sauƙin a kama shi da haka fiye da ba malami ba. Dalilina na uku na ƙarshe da malami  ya cancanta ya jagoranci al’umma shi ne, shi malami kullum hidimar al’uma yake ta ilimantar da su da kyautata musu. Don haka, waɗannan dalilai uku ne ya sa malamai ya kamata su jagoranci al’umma. Amma jahilai da wasu ‘yan bokon da ma masu wani ra’ayin daban, su ne suke ganin bai dace malami ya jagoranci al’umma ba. Ina ganin na amsa waɗannan tambayoyi naka wasalama alaikum warahmatulahi ta’ala wa barakatuhu. 

Malam, mun gode.
Ni ma na gode, bissalam.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *