JIBWIS ta yi babban rashi a jihar Nasarawa

Allah Ya yi wa shugaban Majalisar na JIBWIS mai hedikwata a Jos, Sheikh Sirajo Alhaji Sabo rasuwa.

Malam ya cimma ajalinsa ne sakamakon haɗarin mota da ya rutsa da su a kan hanyarsa ta zuwa garin Danaturu inda zai gabatar da Tafsirin Ramadan na wannan shekarar.

Baya ga Sheikh Sirajo, ƙarin waɗanda suka rasu a haɗarin har da Malam Adam Muhammad Damaturu, Mataimakin Sakataren Tsare-tsare na Ƙasa (F.A.G) da matar Alaramma Hafiz Idris Isa Lafiya mai jan baƙi.

Bayanan JIBWIS reshen jihar Yobe sun nuna gobe Litinin za a yi jana’izar marigayan da misalin ƙarfe goma na safe a garin Potiskum a Masallacin Adamu Waziri (JIBWIS Juma’at Mosque 2, Potiskum).

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *