Kawu Sumaila ya lashe zaɓen Sanatan Kano ta Kudu

Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano

Ɗan takarar Sanatan Kano ta Kudu a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar NNPP, Suleiman Abdurrahaman Kawu Sumaila OFR, ya sami nasarar lashe zaɓen sa na zama Sanatan Kano ta Kudu a Majalisar Dattijai ta Tarayya,

Farfesa Ibrahim Barde, wanda shi ne babban baturen zaɓe na shekarar 2023 a yankin, shi ne ya bayyana samakon zaɓen a cibiyar tattara sakamakon da ke ƙaramar hukumar Rano.

“Kawu Sumaila na jam’iyyar NNPP ya samu ƙuri’u 319,857 inda abokin hamayyarsa Kuma sanata Mai barin gado Kabiru Gaya ya Sami luri’u 192,518.

“Saboda haka bayan cika dukkan ƙa’idojin zaɓe, Abdurrahaman Kawu Sumaila ya yi nasarar zama sanatan Kano ta Kudu a zaben 2023,” inji Barde.