Mai neman zama gwamnan Neja a APC, Mohammed Malagi, ya yi alƙawarin kula da haƙƙin mata da matasa

  • Mawallafin na jaridun Blueprint da Manhaja ya bada gudunmawar naira miliyan 43 da motocin safa 31 ga jam’iyya a jihar

DAGA WAKILIN MU

Mawallafin jaridun Blueprint da Manhaja, wanda ke neman tsayawa takarar gwamnan Jihar Neja a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar APC, Alhaji Mohammed Idris Malagi, ya yi alƙawarin cewa idan har ya ci zaɓe zai kula da haƙƙin mata da matasa a gwamnatin sa.

A yayin da ya ke jawabi ga shugabannin jam’iyyar lokacin da ya kai masu ziyara a ranar Talata a Minna, Malagi ya ce: “Za mu ci gaba da bai wa mata da matasa kyakkyawar kulawa kamar yadda ya kamata.

“Babu yadda za a yi mu cimma nasarar gudanar da mulkin dimokiraɗiyya ko wani tsari na siyasa ba tare da mun sako mata da matasa a cikin tafiyar ba. Mu na goyon bayan mata da matasa. Mun yarda da ku ainun.”

Bayan ya kira kan shi da “wanda ya taka muhimmiyar rawa wajen kafa jam’iyyar APC tun daga farkon ta”, sai kuma ya ce, “Na tsaya nan a gaban ku ne a yau saboda duk mun zaɓi mu kasance masu biyayya, masu tsare gaskiya, kuma nagartattun ‘ya’yan gagarumar jam’iyyar mu ta APC. Ba kawai kirarin jam’iyya ko tutar ta ba ne su ka haɗe mu a waje guda ba, a yau mun zama babban gida na ƙasa baki ɗaya. A Jihar Neja, APC ce jam’iyyar da ta fi kowace jam’iyya da mu ka gani tun daga 1999.”

Malagi ya kuma yaba wa gwamnan jihar, wato Alhaji Abubakar Sani Bello, saboda yadda ya taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da cewa APC ta zama gagarumar jam’iyya a Jihar Neja.

Haka kuma ya taya murna ga shugaban APC na jihar, Alhaji Haliru Zakari Jikantoro, da kuma shugabannin ta na matakan yanki da ƙananan hukumomi da wad-wad saboda nasarar zaɓe da kuma rantsarwa da su ka samu kwanan nan.

Ya bayyana zaɓen Jikantoro a matsayin ciyaman ɗin jam’iyyar na jiha da cewa “sabon alfijir ne da ya keto na ingantantacciyar dimokiraɗiyya a Jihar Neja.”

Ya ƙara da cewa, “Ina addu’ar Allah ya sa wannan nasara ta zama abin da zai kawo ƙarin nasarori a rayuwa da kuma harkar siyasa.”

Alhaji Mohammed Malagi ya faɗa wa shugabannin jam’iyyar cewa: “Yanzu mulkin dimokiraɗiyyar jam’iyya ya na hannun ku. Mu na da tabbacin ku na da basirar yi wa Jihar Neja aikin da za a yi alfahari da ku.”

Ya tunatar da shugabannin cewa shi ma ya jima ya na tallafa wa APC a Jihar Neja saboda ya yi amanna da cewa ita ce “jam’iyyar jama’a daga kowane ɓangare na rayuwa.”

Ya ce, “Shi ya sanya na ke tabbatar da ganin ana ɗorawa a kan nasarorin da ta ke samu, tare da biyan kuɗin hayar ofisoshin ta na jiha da na yankuna. Ba zan gaji ba a wannan hoɓɓasa na nuna biyayya. Kuma zan ci gaba da tallafa wa ayyukan jam’iyya a duk lokacin da aka buƙace ni.

“Ya shugaba, mun zo nan wurin ne a yau da niyyar mu taya ku murna sannan kuma mu ba ku cikakkiyar girmamawa, mu karrama dukkan shugabannin jam’iyya yadda ya kamata saboda mu ‘ya’yan APC ne, mu iyalai ne abin sha’awa.

“Su kuma masoya tare da masu taya Malagi murna, waɗanda su ka zo nan a yau domin mu yi taron murnar nasarar APC tare, ina maku marhabin kuma ina gode maku saboda tsantsar amincin ku da soyayya da kuma goyon bayan da ku bayarwa ba tare da gajiyawa ba.”

A lokacin wannan ziyarar dai, mai neman zama ɗan takarar ya bayyana “wata ‘yar gudunmawa” don samun cigaba, haɗin kai da ɗorewar jam’iyyar, inda ya ba ta kyautar naira miliyan 43 tare da motocin safa guda 31.

Malagi ya ce ya bada kyautar ne saboda a ƙara ƙarfafa jam’iyyar a jihar.

Yadda aka raba gudunmawar shi ne: motocin safa ƙirar Sharon guda 3 da kuma naira miliyan 15 ga sakatariyar jam’iyyar ta jiha, sai mota 1 ƙirar Sharon haɗi da kuɗi naira miliyan 1 ga kowane ofishin yanki na jam’iyya.

Haka kuma ya ba ofishin jam’iyya a kowace daga cikin Ƙarananan Hukumomi 25 na jihar kyautar mota Sharon haɗi da naira miliyan 1. Kuɗin sun kama naira miliyan 25 da kuma motocin Sharon guda 25 kenan.

Malagi ya yi amfani da wannan dama ya miƙa ta’aziyyar sa ga al’ummar jihar bisa rasuwar tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Isah Ibrahim Ladan, wanda ya ce “ƙwararren ma’aikaci ne.”

Haka kuma ya jajanta wa shugabannin jam’iyyar tare da addu’ar Allah ya ba su haƙurin jure wannan babban rashi.

Malagi ya kuma bayyana alhini kan kisan killar da ‘yan ta’adda su ka yi wa wasu jami’an Hukumar Rundunar Tsaron Nijeriya (NCDC) a Shiroro kwanan nan, ya ce, “Allah ya jiƙan su da rahama.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *