Nasarawa 2023: Kada ku bari a ruɗe ku da siyasar addini – Yakubu Maidoya

Daga JOHN D. WADA, Lafia

A ci gaba da ziyartar lungu-lungu da sako-sakon Jihar Nasarawa da ɗan takarar Jam’iyyar NNPP na kujerar gwamnan jihar, alhaji Abdullahi Yakubu Maidoya, ke yi a yanzu don gudanar da kamfen ɗinsa, ɗan takarar ya yi kira musamman ga mabiya addinai daban-daban, musamman Musulmi da Kiristoci cewa kada su bari wasu gurɓatattun ‘yan siyasa waɗanda ke son kansu kaɗai marasa kishin ƙasa suna ruɗin su da batun addini don cimma mummunar burinsu a wannan lokacin zaɓe.

Honorabu Abdullahi Yakubu Maidoya ya yi wannan kira ne a jawabinsa a lokacin da ya gana da wasu shugabannin Ƙungiyar Mabiya Addinin Kirista ta Ƙasa (CAN), reshin Ƙaramar Hukumar Nasarawa a jihar don neman goyon bayansu a lokacin zaɓen.

Ɗan takarar ya ce, a yanzu lokaci ya yi da ya kamata mabiya addinai daban-daban a jihar da ƙasa baki ɗaya su gane cewa waɗannan gurɓatattun ‘yan siyasar sukan fake ne da addinin wajen neman ƙuri’un al’umma sannan da zarar suka samu biyan buƙatunsu sai su riƙa sace dukiyar al’umma ba tare da yin la’akari da batun addinin kuma ba.

Acewarsa, za a iya yin misali da tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan wanda aka ta nuna masa adawa cewa shi ba Musulmi ba ne har aka cire shi a kujerar shugaban ƙasa.

Sai kuma ga shi a yanzu da aka ba Muhammadu Buhari wanda Musulmi ne da musulmin da kiristoci kowa na ɗanɗana kuɗarsa.

Ya ci gba da cewa “Abin da nake so ku sani shi ne a duk lokacin da waɗannan ‘yan siyasa marasa kishin ƙasa ke satar dukiyarku kansu a haɗe yake babu batun addini a tsakaninsu.

“Amma da zarar lokacin zaɓe ya gabato sai su riƙa fakewa da batun addini suna ruɗar ku don samun biyan buƙatunsu,” Inji shi.

Maidoya ya yi amfani da wannan dama wajen gabatar da sauran ‘yan takarar jam’iyyar ta NNPP da ke neman matsayi daban-daban kuma a matakai mabambanta inda ya buƙaci al’ummar yankin da su zuba musu ƙuri’a yauin zaɓe mai zuwa.

Muddin aka zaɓe shi ya kafa gwamnati a jihar, zai gudanar da ayyukan cigaban alumma a kowane fannin jihar tare da kyautata rayuwar jama’a yadda ya kamata.

Daga nan ya yaba wa shugabannin CAN na yankin dangane da irin kyakkyawar tarbar da suka da ya samu.

A nasu ɓangaren, shugabannin CAN na Nasarawa ƙarƙashin jagorancin Fasto Morris Aloysius, sun yaba da dalon kamfen ɗin ɗan takarar ba tare da nuna bambancin addini ko ƙabilanci ba.

Kana sun tabbatar masa da cewa suna tare da shi ɗari bisa ɗari.

Daga bisani, Maidoya ya ziyarci al’ummomi daban-daban da ke yankin ƙaramar hukumar ta Nasarawa da suka haɗa Hausawa da Idoma da Agatu da Kwandara da Igbo da Akiri da Afo da sauran su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *