Nijeriya za ta soma fitar da shinkafa zuwa Masar duk da ƙarancin abincin da yake damun ƙasar

Daga AMINA YUSUF ALI

A yayin da ƙasar Nijeriya take fama da matsanancin ƙaranci da tsadar kayan abinci kama daga hatsi har kayan masarufi, musamman shinkafa wacce aka fi amfani da ita a kodayaushe. A yanzu haka ƙasar ta ƙulla wata yarjejeniya da ƙasar Masar don ta dinga kai musu shinkafa.

A yanzu haka dai ƙungiya mai zaman kanta ta manonman shinkafa a Nijeriya (RIFAN) da wani kamfani mai zaman kansa a Nijeriya sun rattaba hannaye a wata yarjejeniyar fahimtar juna tsakaninsu da ƙasar ta Misira don a fara sayar musu da shinkafar da aka noma a gida Nijeriya.

Wannan jawabi ya fito ne daga bakin ɗaya daga ɓangarorin da aka yi yarjejeniyar wato Mataimakin Manajan Daraktan kamfanin shinkafa mai zaman kansa na Tiamin, Mista Aliyu Ibrahim a Abuja.

A cewar Mista Aliyu, wannan yarjejeniyar ta ta’allaƙa ne a kan tana da burin girbe shinkafa ingantacciyar mai yawa daga ƙungiyar ta RIFAN, wacce daga bisani sai kamfanin Tiamin ya gyara ta a sanya a buhunhuna a sayar a Nijeriya da wajenta, wato dai inda aka hara shi ne Misira.

A cewar sa, wannan kwangila da aka rattaba wa hannu an ƙulla ta ne na tsahon shekaru biyu. Kuma an qulla yarjejeniyar a kamfanin sarrafa shinkafar dake Bauchi.

Kuma a cewar sa, ana noma shinkafar ne a a filin noma da ya kai girman kadada 10,000 a garin Udubo, dake jihar Bauchi.

Daga ƙarshe, ya bayyana cewa, sun samu gudanar da wannan aikin noman shinkafa ne ta hanyar bashin Babban Banki Nijeriya (CBN). Inda ya bayyana cewa kusan karo shida kenan Kamfanin shinkafar yana katari da samun rancen kudi daga Gwamnatin Tarayya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *