Ogun: Gwamna Abiodun ya ƙaddamar da Amotekun

Daga WAKILINMU

A matsayin wani mataki na ci gaba da yaƙi da matsalar tsaro a Jihar Ogun, Gwamnan jihar, Dapo Abiodun, ya ƙaddamar da shirin bada tsaro na cikin gida, wato Amotekun.

Da yake jawabi yayin ƙaddamawar, Gwaman ya ce ba a samar da Amotekun don ta zama kishiya ga sauran hukumomin tsaro ba, face don ƙarfafa wa fannin tsaron jihar.

Ya ce gwamnatinsa za ta bai wa shirin Amotekun cikakken haɗin kai tare da samar masa da kayan aikin da yake buƙata don cim ma manufar kafa shi.

Tuni Gwamnan ya nuna alamar mara wa shirin baya ta hanyar bada gudunmawar kayan aiki da suka haɗa da; motoci da babura da na’urorin sadarwa da sauransu.

Yayin taron, an ga Gwamna Abiodun ya ƙawata fitaccen marubucin adabin nan, wato Farfesa Wole Soyinka, da unifam a matsayin Babban Jami’i na Musamman na Amotekun.

Idan dai za a iya tunawa, a Yunin 2019 ne aka gudanar da wani babban taro kan sha’anin tsaro a shiyyar Kudu-maso-yamma inda jihohin shiyyar su shida suka yi ittifakin kafa shirin tsaro na Amotekun da zummar yaƙi da matsalolin tsaron da suka addabi yankin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *