Ogun: Kwastam ta kama shinkafar ƙetare buhu 5,931, tabar wiwi buhu 290

Daga WAKILINMU

A matsayin wani mataki na ci gaba da kare rayuwar matasa daga barin faɗawa garari, Hukumar Yaƙi da Fasa-ƙwauri ta shiyyar Ogon I ta matse ƙaimi wajen yaƙi da fasa-ƙwaurin miyagun ƙwayoyi da sauran kayayyakin da aka haramta shigo da su cikin ƙasa.

Da wannan ne hukumar kwastam ɗin ta ce lallai aikin haɗin gwiwar da suke yi tare da Hukumar Yaƙi da Sha da Safarar Muggan Ƙwayoyi (NDLEA) a shiyyar Ogun ya haifar da ɗa mai ido.

A cewar shugaban hukumar kwastam na shiyyar, Comptroller PC Kolo, sun samu nasarar kama tabar wiwi har buhu 290 da kuma katan na ƙwayar taramo guda 41, wanda baki ɗaya a ƙiyasce kuɗinsu ya kai mikyan N234.

Kazalika, hukumar ta ce ta sake kama wasu kayayyakin fasa-ƙwauri da dama, ciki har da shinkafar ƙetare buhu 5,931 da manyan jarkoki ɗauke da fetur guda 562 da katan 3,315 na naman kaji da dai sauransu.

Hukumar ta ce ta miƙa waɗanda ta kama da harkar muggan ƙwayoyi ga hukunar NDLEA domin ta yi abin da ya dace.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *