Rawar da uwa ke takawa kan tarbiyyar ’ya’ya

Daga SADIYA GARBA YAKASAI

Za mu ɗora daga inda mu ka tsaya a makon jiya cikin wannan filin naku mai albarka na shafin Tarbiyya a jaridarku ta Manhaja. Kamar yadda na faɗa, iyaye da dama su suke ɓata tarbiyyar yaransu, me ya sa na ce haka? Soyayya! Idan iyaye suka ɗora kacokan ]in rayuwarsu akan yara, to fa tabbas ƙilu za ta ja bau. Shi yaro a kodayaushe ƙwaƙwalwarsa kamar ta kifi ta ke, gani ya ke komai da ta so, dole ya samu, wanda hakan ba ƙaramin illa ba ne. Ya na da kyau a nuna ma sa abinda ta dace, ba son ransa ba. Hakan zai ba shi ƙwarin gwiwar cewa, shi da zai wa kansa gata, shi zai samar wa rayuwarsa ƙima, don ya fito a mutumin kirki.

Kayan maye
Yanzu waɗannan abubuwa da su iyaye ke kuka, saboda yanzu matasanmu wannan rayuwar suka sa a gaba mawuyaci ne yanzu cikin kaso goma na matasa ka samu kaso huɗu lafiyayyu. Takaicin shine, ba babba ba yaro, ba mace ba namiji, abun ya zama ruwan dare; kayan maye sun baibaye yara.

Me ya ke jawo shaye-shaye?
A lissafina ko na ce tunanina, abun da ke jawo wannan miyagun abubuwan su ne kamar haka:

Rashin sa ido na uwa: Muddin uwa za ta saki yaro sakaka ya fita inda ya so, ya kuma dawo sanda ya so, to ba shakka uwa ta ɗauki ɗamarar lallacewar ɗanta.

Rashin aikin yi: Rashin aiki ya jawo yara matasa ta yawa fadawa cikin wannan ɗabi’a ta shaye-shaye. Muddin yaro ba ya zuwa makaranta ko sana’a ko wani abu dai da zai sa yaro cikin uzuri, wanda zai janye yaro daga faɗa wa hali maras kyau, wato su ne, aiki, karatu ko sana’a, to tarbiyyarsa za ta iya gurɓata. Wadannan sune babban gata da iyaye za su yi wa yaro, wato faɗa wa wannan ɗabi’a, tunda maye ba abun da bai faɗawa. Akwai da dama da rashin aiki da sana’a ya ja musu faɗa wa shaye-shaye, saboda ƙwaƙwalwarsu kawai na zayyana musu lissafi maras ma’ana a matsayin abu mai kyau. Duk illar shaye-shaye ke jawo waɗannan abubuwan.

Kulob: Wannan ma yana daɗa taɓarbara rayuwar yaranmu. Daga zarar yaron ki ya fara zuwa gidan kallo ko gidan dambe, to ki san yaronki ma yana zuwa kulab. Muddin zai raba dare a waje, to ki bincika ki gani daga ina ya ke, me ya ke yi a irin wannan daɗewar daren? Idan ki ka samu ya fara zuwa waɗannan guraren, to fa sai kin yi da gasken-gaske kafin ki shawo kansa ya daina. Ba kuma namiji kaɗai ke zuwa gurin ba, yara mata ƙanana na zuwa. Daga samari ko ƙawaye ake samun masu tura musu wannan aƙida ta zuwa kulab. Muddin baki ɗauki mataki ba, to fa kin gamu da gamon rashin kwanciyar rai.

Rashin ilimi: Wannan ma babban ƙalubale ne a rayuwar yaranmu. Muddin aka ce yaro ba shi da ilimi, to babbar barazana ta shiga, don idan da ilimi, to fa wani abun yaro ba zai yi ba da kansa, saboda ya san illar hakan. Ya na da kyau iyaye su yi ƙoƙarin nuna wa yara mahimmancin ilimi da kuma abun da ya ke taimakawa a rayuwarsa.

Uwa mai ganin laifin uba ga tarbiyyar ɗansa: Ikon Allah don me ke uwa za ki hana uba ya yi wa ɗansa faɗa? Ikon Allah! To, ke ki na nufin kin fi, don ɗan shi uba ba ya son shi ne? Ki kula wallahi ba ki da hurumin hana uba ya yi abun da ya ke so da rayuwar ɗansa. Ya ma fi ki haƙƙi a kan ɗansa. Babu ruwanki da horo da uba zai wa ɗansa. Ke kawai haƙƙinki ki ba wa mijinki goyon bayan yi wa ɗansa tarbiyya. Da zarar kin rusa wannan damar, to ki sani kin yi wa kanki illa wallahi. Ke ba a son ɗanki, ke an tsani ɗanki, hummm ba za ki gane cutar ɗan naki ki ke yi ba, ba za ki gane cutar kanku ki ke yi ba, sai sanda kowa ya guje ki, ya guji ɗan naki, kuma ki ka kasa ba wa ɗan naki tarbiyyar! Uwargida, ki tuna dai da karin maganar Bahaushe da ya ce itace tun yana ɗanyensa ake tanƙwara shi, kuma ka so naka duniya ta ƙi shi, ka ƙi naka kuma duniyar ta so shi. Ke a gurinki wanne ki ka zaɓa? Kawai ki bari duniyar ta gaya ma sa gaskiya, shi ya fi dai. Don Allah iyaye mata mu gaya ma kan mu gaskiya, don wallahi uban da zai so ɗansa ya wulaƙanta, kuma komai mugun halinsa yana son ɗansa, ba ke kaɗai ki ke son sa ba. Duk wanda zai guji ɗansa, to ba shi yake ƙi ba, mugun halin sa yake ƙi.

Zaman aure: Duk uwar da ta aurar da ɗiyarta, to ta tabbata ta koya mata tarbiyyar zama da miji, ba ki sakaka ki saki ɗiyar taki ba. Idan ba ki koya mata komai ba, to ki na cikin ruɗun rayuwa da kashe wa ɗiyarki rayuwa. Yanayin yadda ki ka ba wa ɗiyarki tarbiyya, yanayi rayuwar da za ta yi a gidan mijinta kenan. Don haka uwa ke ki ke da makullin gyara gidan ɗiyarki.

Koya mata yadda za ta rayu da miji: Idan ba ta sani ba, ki sanar da ita, don abun da za ta je ta tarar gidan miji daban da wanda ta samu a gidansu. Kwatanta mata yadda za ta yi wa miji biyayya da ladabi, don gina rayuwa cikin lisilama da jin daɗin zaman gidan mijin; yi na yi, bari na bari. Kuma uwa ta san duk irin abun da ɗiyarta ta gani ki na yi a naki gidan, to shi za ta koya. Idan hali na gari ki ke yi, to ita ma shi za ta yi. Idan na tsiya ki ka yi, shi za ta yi. Shi ne tarbiyyar da ki ka ba ta. Don haka iyaye mata mu dage da kwarkwanta abun da za ki yi wa naki mijin, domin ta nan ita ma za ta yi a nata gidan.

Zamantakewar miji da mata: Wannan ita ce dangantaka mai kyau. Ki karanci halayyar da abun da ya ke so, wanda ba ya so, kyautatawa da kulawa. Shi namiji a kullum kamar yaro ya ke a gurin mace; ya na so ya ga ki na nuna ma sa kula da soyayya, sannan ki ɗora da masa da shagwaɓa. Idan har kin gane abun da mijinki ke so, to wallahi lafiya za ku zauna, amma idan kin nuna masa faɗin rai, to za ku yi ta ɗauki ba daɗi. Idan aka samu haka, sha’ani ya ɓaci. Ke da kanki za ki gyara gidanki, domin ke ce mai riƙe da nama yadda ki ka so, haka za ta faru. Amma idan kin sa girman kai ko rashin ladabi, to ki na ruwa! Sai ki tarkowa kanki rigima ta rashin jin da]in aure ko kuma a zabgo miki kishiya. Duk mace da ta rasa kan mijinta, to ta binciko yadda ta ke tafiya da gidanta, don dai shi namiji haka kawai ba zai juya miki baya ba dalili ba.

Za mu ɗora a sati na gaba tare da fatan Allah ya sa mu dace. Masu turo da tambayoyi da yabawa muna godiya. Allah ya sa mu amfani da abun da aka samu. Wa’assallam.