Shugaban Ƙasar Sin ya miƙa saƙon taya murna gabanin bikin girbin amfanin gona na manoman ƙasar

Daga CMG Hausa

Babban sakataren kwamitin ƙolin JKS kuma shugaban ƙasar Xi Jinping, ya mika sakon taya murna a madadin kwamitin ƙolin JKS, ga daukacin manoman ƙasar, da sauran waɗanda ke gudanar da ayyuka daban-daban masu nasaba da noma da raya karkara, gabanin bikin girbin amfanin gona na manoman ƙasar Sin karo na 5.

Xi, ya kuma jaddada muhimmancin tabbatar da ci gaba wajen farfado da ƙauyuka, da aiwatar da matakan samar da wadata, da jin dadin rayuwa, da kyakkyawan muhalli ga mazauna yankunan karkara.

Mai fassara: Saminu Alhassan

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *