Ta yaya manufar “ƙasa ɗaya, amma tsarin mulki iri biyu” ta cimma nasarar da aka gani a Hong Kong?

Daga CMG HAUSA

“A cikin shekaru 25 da suka gabata, a ƙarƙashin cikakken goyon baya daga ƙasar uwa, da kuma ƙoƙarin haɗin gwiwa da gwamnatin yankin musamman na Hong Kong, da ma dukkan ɓangarorin al’ummar yankin suke yi, manufar ‘ƙasa daya, amma tsarin mulki iri biyu’ ta samu nasarar da aka sani a Hong Kong. “

A ranar 1 ga watan Yuli, shugaban ƙasar Sin Xi Jinping, ya gabatar da muhimmin jawabi a wajen bikin cika shekaru 25 da dawowar Hong Kong ƙasar Sin, da kuma bikin rantsuwar kama aiki ta gwamnatin yankin musamman na Hong Kong karo na shida, inda ya nuna yabo sosai kan yadda ake gudanar da manufar “ɗasa ɗaya, amma tsarin mulki iri biyu” a Hong Kong.

Da ƙarfe 0:00 na ranar 1 ga watan Yulin shekarar 1997, gwamnatin ƙasar Sin ta dawo da ikon mallakar yankin Hong Kong, kuma a hukumance aka ƙaddamar da sabon tsarin siyasa na “ƙasa ɗaya, amma tsarin mulki iri biyu”. A cikin shekaru 25 da suka gabata, yankin Hong Kong ya shawo kan ƙalubale daban-daban, kuma an tabbatar da matsayinsa na cibiyar hada-hadar kuɗi, da ta jigilar kayayyaki, da ta cinikayya ta ƙasa da ƙasa, kana mazauna Hong Kong na samun ikon demokuraɗiyya, da ‘yancin kai da ba a taba ganin irinsa ba, kuma an kyautata jin daɗin jama’a sosai.

Ga misalin, jimillar GDP na Hong Kong, da matsakaicin GDP na kowane mutum sun ƙaru, daga dalar HK tiriliyan 1.37 da dalar HK dubu 192 a shekarar 1997, zuwa dalar HK tiriliyan 2.86 da dalar HK dubu 387 a shekarar 2021. Kaza lika yawan kuɗin musaya da aka tanada ya ninka sau 5 bisa na shekaru 25 da suka gabata.

Hong Kong ya samu gagarumar nasara a cikin shekaru 25 da dawowarsa ƙasar Sin, wanda ke nuna cewa, manufar “ƙasa ɗaya, amma tsarin mulki iri biyu” ta Hong Kong ta samu gagarumar nasara, a cikin shekaru 25 da dawowar yankin, kana hakan ya nuna cewa, manufar “ƙasa daya, amma tsarin mulki iri biyu” ta jure duddubawa daga yunƙurin aikatawa.

Wadda kuma ke dacewa da moriyar ƙasa, da babbar moriyar al’umma, da babbar moriyar Hong Kong da Macau, kuma hakan ya samu goyon baya daga wajen Sinawa fiye da biliyan 1.4, da goyon bayan bai daya na mazauna Hong Kong da Macau, har ma ya samu amincewar ƙasashen duniya baki daya. “Irin wannan tsarin mai kyau, babu wani dalili na canza shi, kuma dole ne a gudanar da shi cikin dogon lokaci!”

Mai fassara: Bilkisu Xin

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *