Tsohon Mataimakin Gwamnan Ekiti ya mutu a ranar zaɓe

Daga BASHIR ISAH

Allah Ya yi wa Mataimakin Gwamnan Jihar Ekiti na baya-bayan nan, Otunba Bisi Egbeyemi, rasuwa a ranar Asabar da ake gudanar da zaɓen gwamnoni da na majalisar jihohi.

Egbeyemi ya rasu ne da safiyar Asabar a wani asibiti da ke Ado-Ekiti, babban birnin jihar.

An haifi marigayin ne ran 8 ga Mayu, 1944, inda ya bar duniya yana da shekara 79.

A halin rayuwarsa, lauya ne shi kuma ɗan siyasa.

Ya taɓa riƙe matsayin Shugaban Ƙaramar Hukumar Ado Ekiti daga 1992 zuwa 1993, kafin daga bisani ya zama Mataimakin Gwamnan jihar ga Gwamna Kayode Fayemi, daga 2018 zuwa 2022.

Sai dai babu cikakken bayani kan abin da ya yi ajalin marigayin ya zuwa haɗa wannan labari, kuma ɗaya daga cikin ma’aikatansa ne ya ba da sanarwar rasuwar tasa.