Ukraine ta yi musayar fursunoni da Rasha ciki har da Ba’amurke

Daga SANI AHMAD GIWA

Ukraine ta ce, ta samu nasarar karɓo wani ɗan Ƙasar Amurka da kuma wasu sojojin ƙasarta 64 a wani sabon shirin musayar fursunoni da ta yi da Rasha.

“Sojoji 64 na sojojin Ukraine da suka yi yaƙi a Donetsk da Lugansk a ƙoƙarin kare birnin Bakhmut na hanyar komawa gida,” inji babban hafsan hafsoshin fadar shugaban Ƙasar Ukraine Andriy Yermak.

“Haka kuma an samu nasarar kuvutar da wani ɗan Ƙasar Amurka da ya taimaka wa mutanenmu,” a cewar Suedi Murekezi.

Fadar White House ta tabbatar da sakin wani ɗan Ƙasar Amurka.

“Tabbas muna maraba da labarin. Amma saboda dalilai na sirri, haƙiƙa ba zan iya yin wani cikakken bayani game da wannan mutumin ba,” inji kakakin Kwamitin Tsaron Amurka John Kirby, ga manema labarai.

Kamfanin dillancin labaran TASS na Ƙasar Rasha ya bayar da rahoton cewa, an kama Murekezi a yankin gabashin Donetsk na Ƙasar Ukraine a watan Yuni, inda aka tuhume shi da laifin halartar zanga-zangar ƙin jinin Rasha da kuma haddasa ƙiyayyar ƙabilanci.

TASS ya ce, Murekezi haifaffen Rwanda ne kuma ya koma Amurka tare da iyalansa a shekarar 1994. Lauyansa ya ce, Murekezi ya yi aiki a wani gidan rawa a birnin Kherson kuma ya musanta cewa, wanda yake karewa ɗan gwagwarmaya ne.

Dakarun Rasha sun ƙwace birnin Kherson jim kaɗan bayan da suka mamaye Ukraine a watan Fabrairu, amma sojojin Ukraine sun sake ƙwace garin, tun daga lokacin hare-haren Rasha suka zafafa.

Hukumomin Ukraine sun ce, yankin da ake gwabza faɗa tun bayan ƙwato Kherson shi ne yankin Donetsk inda sojojin Rasha suka kwashe watanni suna ƙoƙarin ƙwace Bakhmut.