Waƙa: ALLAH JIƘAN SARKI ADO

Daga KHALID IMAM

Lokacin da muke da sarki,

Kada sarki a tafki,

Goro daushe mai kamala,

Wanda kowa ke muradi,

Mararin ya gani a kullum,

Kowa a cikin ƙasarmu,

Kewayenta da duniya kaf,

Yasan darajar Kanawa.

Lokacin Sarkinmu Ado,

Kano da dukkan Kanawa,

Sun yi ƙima babu shakka,

Lokacin babban sadauki,

Dodo namijin mazaje,

Ado ɗan abdu zaki,

Dukkanin jama’ar Arewa,

Sun san a Kano da sarki.

Lokacin sarkinmu Ado,

Ba ma a Jihar Kano ba,

Dukkanin mutumin Arewa,

Yai alfahari da tsauni,

Wanda ba a yi wa dundu,

Lokaci na giye a sarki,

Dukkan wani ɗa Bahaushe,

Jinjina ya yi wa Ado.

Ado ɗan abdu mashi,

Lokacin da ya ke da ransa,

Ya sawa dukkan Kanawa,

Rigar daraja da ƙima,

Duk inda ya sa ƙafarsa,

Kowa yasan da gaske,

Zaki ya gani karimi,

Mai mutunci mai halarci.

Allah Ka jiƙan Niƙatau,

Zuma kowa yana so,

Giye da ya saba tunga,

Sai ya toye matsafa,

Wanda ba a yi wa wargi,

Wanda ba a yi wa wauta,

Takawa mai amana,

San Kano Adon Kanawa.