Wasu attajiran duniya sun roƙi ƙasashe su ƙara mu su haraji

Fiye da attajiran duniya 100 ne suka miƙa buƙatar ganin gwamnatoci na karɓar haraji a hannunsu fiye da kowa, a daidai lokacin da wani rahoto ke ganin harajin attajiran duniya na dala tiriliyan 2.52 a shekara guda zai taimaka wajen wadata duniya da alluran rigakafin Korona.

Cikin wata buɗaɗɗiyar wasiƙa da attajirai 102 suka aika wa taron tattalin arziki na Davos wanda ke gudana ta bidiyon ‘intanet’, sun bayyana damuwa kan yadda tsarin karɓar harajin da ake amfani da shi a yanzu yake ƙara arzurta attajirai.

Wasiƙar wadda attijaran suka yi wa laƙabi da ‘‘Ku karɓi haraji daga gare mu attajirai yanzu’’ ta isa ga taron na Davos ne a dai dai lokacin da rahoton ‘Oxfam’ ke nuna yadda za a iya tattara haraji daga hannun attajiran duniya da yawansa ya kai dala tiriliyan 2 da biliyan 52 a shekara guda wanda zai iya wadata duniya da alluran rigakafin Korona baya ga cire mutane biliyan 2 da miliyan 300 daga talauci.

Wasiƙar ta ce, wajibi ne ƙassahen duniya su yi adalci wajen karɓar haraji daga hannun attijarai yadda ya kamata, saɓanin tsarin da ake amfani da shi wajen ƙara arzurta mawadata da kuma talauta talakawa.

Attajiran sun miƙa wannan wasiƙa ne kwanaki biyu bayan wani rahoton ƙungiyar Oxfam ya sanar da yadda attajiran duniya 10 suka ruɓanya arzikinsu a lokacin annobar Korona da dala tiriliyan 1 da rabi karon farko da aka ga irinsa a shekaru 2.

Wasiƙar attajiran ta ci gaba da cewa, la’akari da halin da Korona ta jefa duniya, wajibi su bayar da haraji fiye da yadda suke bayarwa a baya don ceto miliyoyin rayukan da ke fuskantar barazana.

Attajiran da ke da hannu a wasiƙar neman ƙarin harajin akansu sun ƙunshi wasu daga Amurka da Canada da Jamus da Birtaniya da kuma Denmark baya ga attajiran ƙasashen Norway da Austria da Holland da kuma Iran.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *