Yaƙi Da Matsalar Tsaro: Zulum ya ƙalubalanci shugabannin tsaro su kyautata alaƙa da takwarorinsu

Daga AISHA ASAS

Gwamnan Jihar Barno, Babagana Umara Zulum, ya ƙalubalanci sabbin shugabannin tsaro da su assasa kyakkyawar alaƙar aiki a tsakaninsu da ƙasashen da Nijeriya ke maƙwabtaka da su, wato Chadi da Kamaru da kuma Nijar.

Kazalika, ya shawarci manyan hafsoshin da su kasance masu haƙuri da kuma sauraron jama’a a halin aiwatar da ayyukansu.

Gwaman ya faɗa wa jami’an haka ne sa’ilin da ya karɓi baƙuncinsu a fadar gwamnatin jihar a Lahadin da ta gabata yayin da suka yi ziyarar aiki ta farko a jihar.

Shugaban tsaro Major-General Leo Irabor, shi ne ya jagoranci takwarorinsa Major-General Ibrahim Attahiru da Rear Admiral Awwal Zubairu Gambo da Air Vice Marshal Isiaka Oladayo Amao yayin ziyarar.

Da yake jawabi, Gwamna Zulum ya buƙaci shugabannin da su hanzarta hada kai da sojojin ƙasashe maƙwabtan Nijeriya, tare da kyautata dangantaka a tsakani domin yin aiki tare wajen ci gaba da yaƙi da harkokin ‘yan bindiga.

Haka nan, ya bai wa sojojin tabbacin samun goyon bayan gwamnatinsa domin taimaka musu wajen samun nasara a ayyukansu.

Tun farko, da yake magana a madadin tawagarsa, Major-General Leo Irabor, ya bai Zulum tabbacin cewa a shirye suke su yi aiki. Kana ya yi kira ga ɗaukacin al’umma da a fahimci yanayin aikinsu a fagen yaƙi da ta’addanci sannan a ba su haɗin kan da suke buƙata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *