WASIƘU: Yajin aikin ASUU: Ina ɗalibai za su sa kansu?

*Shigo da gurɓataccen fetur
*Dole a rage kuɗaɗen da ake ba shugabanni da ’yan majalisar Nijeriya

Assalamu alaikum. A safiyar ranar Litinin ne Ƙungiyar Malaman Jamio’i ta Nijeriya, wato ASUU, ta sanar da fara yajin aiki na gama gari na tsawon wata guda, yajin aikin da ta kira da na gargaɗi bisa zargin gazawar gwamnati a cika alƙawuran da ta yi wa ƙungiyar na samar da kuɗaɗen gudanarwa ga jami’oin na gwamnati.


A gaskiya idan za mu duba zuwa ga wannan al’amari za mu cewa laifin gwamnati ne, a matsayinmu na ɗalibai, kuma hakan na matuƙar kawo cikas a ɓangaren karatun ɗalibai.

Yajin aiki a tsakanin malaman jami’o’in gwamnatin Nijeriya, kusan ya zama ɗan kullum, domin a shekarar 2020 sai da suka kwashe watani tara suna yajin aiki, duka a kan abu guda na zargin gwamnati a gaza cika alƙawarin da ta yi ma malaman na samar da kuɗaɗen gudanar da jami’o’in.

Malaman sun dage a kan an saɓa masu kama daga kuɗaɗen alawus ya zuwa ga na gudanar da jami’o’in, amma ga wani masani a fanin ilimin boko, na bayyana illar yajin aiki ga karatun jami’a. “Illolin sune, yara ba sa iya kamalla karatunsu a lokacin da ya dace kuma Idan a ka yi rashin sa’a yaro ya koma gida sai ya haɗu da wasu miyagun abokai, sannan iyaye suna cikin ƙunci, kuɗaɗen makarantan da za su biya a cikin shekaru huɗu sai su kai shekaru bakwai.”

Har ya zuwa yanzu, gwamnatin ba ta ce uffan ba a kan wannan yajin aikin ASUU na gargaɗi, domin ta dage kan cewa tana iyakar ƙoƙarinta a kan wannan batu da ya kai wa kowa a wuya, musamman yaran marasa galihu da suka dogara ga jami’o’in gwamnati a ƙasar. Daka yajin da malaman jami’o’in Nijeriyar suka yi suka sha ya tunzura ɗalibai da iyayensu, domin har yanzu ba su kai ga farfaɗowa daga koma bayan da karatun boko ya fuskanta ba, a dalilin ɓullar annobar cutar Korona.

A ƙarshe, muna kira ga gwamnatin tarayya da ta duba halin da ɗalibai ka iya shiga a dalilin irin waɗanda yajin aikin, ta kuma biya Malaman ASUU dukkan haƙƙoƙinsu.
Wassalam.

Daga Mustapha Musa Muhammad, ɗalibi a fannin karatun Injiniyancin Sinadarai (Chemical Engineering) a Jami’ar Federal Polytechnic Kaduna, 09123302968.

Shigo da gurɓataccen fetur

Ƙasa ta yi tir da samun gurɓataccen mai na fetur wanda ga alamu ita ma gwamnatin ƙasarmu ta nuna damuwarta ganin yadda kamfanin mai na ƙasa NNPC ya yi tir da wancen kutse. Zargin ƙasar Baljium da kamfanin Oando na shigo ma ƙasarmu daka da kare duk abun ji yadda a kullum za a kama mai laifi ai ta cece- kuce amma a ƙarshe sai kidi ya kare ga jinjina. Ko shakka ba bu shigowar wancen mai ya janyo matsaloli da dama wanda ya haɗa da lalacewar ababen hawa da kuma ƙarancin shi kamshi man da fatan duk idan wata makamanciyar matsala irin haka ta faru a dunga kamo waɗanda duk su ke da hannu a garzaya da su zuwa kotu kuma ai hukumci na gaskiya kuma da gaske. Ta hakan ne kaɗai gyara zai dunga samun wanzuwa a wannan ƙasa ta mu Nijeriya.

Daga Mukhtar Ibrahim Saulawa Katsina, 07066434519/ 08080140820.

Dole a rage kuɗaɗen da ake ba shugabanni da ’yan majalisar Nijeriya

Ya zama dole a rarrage kuɗaɗen albashi da na alawus-alawus na duk waɗansu zavavvun ’yan siyasa tun daga ƙasa har sama. A nan ina nufin tun daga kansiloli har zuwa shugabannin ƙananan hukumomi, sannan da ’yan majalisar jihohi da majalisun gaba ɗayansu.

Daga nan kuma sai a rarrage kuɗaɗen ’yan Majalisar Wakilai da ta Dattawa. Gaskiya kullum ana cewa talakawan ƙasa suna cikin matsin rayuwa amma an ƙasa ganin yaya al’amarin yake, kuma an yi mirsisi an ki fahimtar ababen da gangan da ganganci. Gaskiyar lamari gwamnati mai ci yanzu tunda ta kama ragamar mulki a shekarar 2015, sai kawai aka wayi gari ta ƙara kuɗaɗen albarkatun man fetur daga Naira 97 zuwa Naira 145 wanda karin ya shallake hankali kuma kananzir da gas duka aka yi musu karin da ya fi na arzikin Kundila.

To, ga masana sun ce an yi haka ne domin tafiyar da gwamnati mafi tsada, wato, ta launin yadda Amurka take yi ‘American System’ to shi ne dalilin ƙarin kuɗin man fetur da dangoginsa. Gaskiya, wannan aƙida ta gwamnati ita ta jawo tashin komai cikin Nijeriya, ta janyo komai ya zama jangwam, kuma talakawa suka shiga cikin wahalolin rayuwa. Abu ne mawuyaci Gwamnatin Muhammadu Buhari ta juyo da baya domin gyara wannan kuskure tunda ’yan siyasar wannan zamani sun rungume ta ce domin lagwadar da ake samu ba wai domin kyautata wa jama’a ba.

Saboda haka, ya zama wajibi kowane ɗan majalisa ya saki rabin kuɗinsa domin taimaka wa ƙasa, haka Shugaban Ƙasa da ’yan majalisarsa da kuma dukkan ministoci. Haka ma gwamnoni da dukkan kwamishinoni da dukkan wanda aka naɗa a siyasance. Gaskiyar lamari, dole Shugaban Ƙasa ya yi iyakar iyawarsa domin ganin duk ’yan Majalisar Wakilai  da na Majalisar Dattawa duk wanda ya karɓi aikin mazabu ‘Constituency Project’ bai yi ba, lallai ya dawo wa gwamnati kuɗaɗenta.

Domin kuwa bai yi aikin ba, saboda haka ya zama dole ya amayar da kuɗaɗen da aka ba shi. Kuma daga ƙarshe rokona ga Gwamnatin Tarayya shi ne a lura da iyakokin ƙasar nan, ba wai kawai a matsa kan shigo da motoci ba ko shinkafa, a’a shigowar baki ratata ba ya zame wa kasa abin alheri domin kashe-kashen bayin Allah sun yi yawa. Saboda haka, dole a hana shigowar bakin haure ta dukkan iyakokinmu duk da an ce daga na gida ake cin yakin gida.

Muhammadu Buhari a matsayinka na Shugaban Ƙasa da gwamnonin jihohi ku tashi tsaye domin ceto ƙasar nan kada ta wargaje, saboda son kai na waɗansu mutane qalilan waɗanda idan ba su samu mulki ba, sai dai Nijeriya ta shiga halin ni-’yasu. Allah Ya tsare, Ilahee Ameen.

Amma dai rage kuɗaɗen albashi da alawus-alawus na waɗanda muka ambata zai zama alheri ga ƙasarmu Nijeriya, sannan a rage kuɗaɗen man fetur da dangoginsa. Haka zai bada damar warware matsalolin Nijeriya da jama’arta.
Wassalam.

Saƙo daga Ahmad Musa, 07041094323.