‘Yan bindiga sun sace malami da wasu mutum huɗu a Yobe

Daga WAKILINMU

Rahotanni daga jihar Yobe na nuni da cewa ‘yan bindiga sun yi garkuwa da wani malamin makarantar firamare tare da wasu mutum huɗu.

Tuni dai rundunar ‘yan sandan jihar ta fito ta tabbatar da aukuwar lamarin a yau Laraba, inda ta ce ‘yan bindiga sun sace Babagana Kachalla wanda malami ne a makarantar Central Primary School, Buni Yadi, tare da wasu mutum huɗu a ƙauyen Madiya da ke yankin Ƙaramar Hukumar Gujba a jihar.

Mai magana da yawun ‘yan sandan jihar, ASP Dungus Abdulkarim, shi ne ya bada tabbacin hakan a Damaturu, babban birnin jihar.

Abdulkarim ya lissafo sauran mutanen da lamarin ya rutsa da su da suka haɗa da: Abubakar Barma da Haruna Barma da Modu Bukar da kuma Hajiya Gana.

Ya ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 8:20 na safe na Talatar da ta gabata amma sai da misalin ƙarfe 10:37 na wannan safiyar labarin hakan ya isa ofishinsu na wannan yankin ta dalilin wani mai suna Mala Boyema.

Ya ƙara da cewa, Boyema ya tsallake rijiya da baya ne yayin harin da ‘yan ta’addar ɗauke da manyan bindigogi suka kai.

Sai dai jami’in ya ce, daga bisani ‘yan bindigar sun sako Hajiya Gana.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *