Ƙalubalen da ke gaban iyaye bayan kisan gillar Hanifa

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Mustapha Bulama wani fitaccen mai zanen barkwanci a jaridu da shafukan sada zumunta, ya yi wani zane a cikin makon jiya inda ya nuna wasu gungun iyaye ko manyan mutane a gefe guda suna ihun sunan Hanifa, wato yarinyar nan ’yar shekara 5 da shugaban makarantar su ya yi wa kisan gilla a Kano, har ma da wani da yake ɗaukar hoton kansa da waya, don ya nuna takaicinsa na abin da ya faru da wannan ƙaramar yarinya.

Daga gefe guda kuma ga wasu yara nan suna kallon su wasu da kwanon bara, wasu cikin tsumma, wasu a ƙanjame babu kyakkyawar kulawa. Yaran sun nuna alamun mamaki kan yadda iyayen nan ke ta kururuwa da ihun takaicin abin da ya faru da wata ƙaramar yarinya, alhalin sun bar nasu yaran babu kulawa, cikin yunwa da tsummokara.

Lallai babu shakka wannan zane ya yi matuƙar jan hankali na da wasu abokan aiki da muka tattauna da su a kai, saboda saƙon da ke ƙunshe a cikin sa, na irin ƙalubalen da yara ke ciki na tagayyara da fuskantar barazanar tsaro a rayuwar su ta yau da kullum, duk kuwa da kasancewarsu yara manyan gobe, waɗanda ake kyautatawa zaton makomar ƙasar nan da ma al’umma baki ɗaya tana hannun su.

Wannan ya tayar da wata ayar tambaya, shin anya iyaye da shugabanni da ke waƙar yara manyan gobe ne sun shirya ba su damar da ta dace da su na karɓar jagoranci da sauwala rayuwar su yadda ya dace da tsarin cigaban rayuwa kuwa? Sakaci, rashin kulawa da nuna ko oho da ake yi da rayuwar yara, babbar barazana ce ga makomar ƙasar nan. Ko iyaye da gwamnati sun sani ko ba su sani ba.

Ihu da kururuwa kan abin da ya faru da yarinya Hanifa Abubakar bai wadatar ba, har sai sauran yara an ba su kulawa da tsaro da ilimin da ya dace a inda ya kamata. Don su yi rayuwa mai inganci kuma cikin aminci, da zai ba su damar zama abin alfahari ga ƙasar nan.

Wannan kuma yana gangarowa ne kan halin da ƙasar ke ciki, na rashin wadata, rashin tsaro da rashin kyakkyawan tsarin tattalin arziki da zai bai wa sauran ’yan ƙasa walwala da tsara abin da zai dace da kyautata rayuwar ’ya’yan su. Yayin da muke kyautata zaton halin ƙuncin rayuwa ce ke sa wasu iyayen bai wa yaransu ingantacciyar rayuwa, a lokaci guda kuma muna zargin wasu iyayen da nuna sakaci da rashin sanin zafin ’ya’yan su ko nuna ko oho da yadda rayuwar su za ta kasance.

A shekarun baya can zamanin hankali na kwance, yara basu san wai su fita su nemi kuɗi a waje ba, ko kuma a tura su koyon sana’a ba. Hatta iyayensu mata ma basu damu da yin wani abin sayarwa a gida ba. Duk iyali sun dogara ne da abin da Uba ko Maigida zai shigo da shi gida daga waje. Kuma daidai gwargwardo ana samun biyan buƙata da rufin asiri. Yanzu kuwa rayuwa ta canja nesa ba kusa ba. Talauci da wahalhalun rayuwa sun tarwatsa iyalai da dama, an fantsama neman abin duniya.

Akasarin magidanta tun sassafe sun fita kasuwa ko neman na cefane, wasu daga cikin su basa ƙara waiwayar gida sai dare ya yi. Su kan su yaran daga sun taso makaranta, musamman masu ɗan wayo, sai ka ga suma sun bazama nema, daga masu zuwa sana’a, koyon aiki, sai masu karan-mota. Sam ba su ma da lokacin da za su zauna su huta a gida, ko kuma su ɗauki littattafan su domin yin bita.

Nunawa yara kulawa da yadda za su dinga ɗaukar rayuwa yana da matuƙar muhammanci, domin yana taimaka masu wajen ƙarin kuzari da cikakkiyar lafiya, da sanya musu buri da kyakkyawan fata. Yaran da ake kula da rayuwarsu sosai, sun fi samun sakamako mai kyau ko a jarabawar makaranta ne.

Yara ba ƙaramar rahama ba ce, ba ka da abokanen sirrin da ya wuce su. Muhimmiyar hanyar da za ka bi ka gyara halayyar yaronka, shi ne ka fara da kanka, domin ka zamar masu abin koyi, kamar yadda Dr. Ellen Rudolph, masaniya a kan rayuwar iyali take cewa, “yayin da iyaye suka kyautata halayensu da zamantakewarsu, nan da nan yaro zai iya tashi da ɗabi’u nagari irin nasu, inda aka fi samun matsala shi ne idan iyaye suka matsa da takurawa da kafawa yaro tsauraran ƙa’idoji, don kada ya lalace, ko rashin samun kulawar da ta dace.”

Ya kamata ku sa ido sosai kan rayuwar yaranku, ku ba su dukkan kulawar da suke buƙata, tun daga tasowar su, lafiyar su, ilimin su, da walwalar su. Ku saki jiki da su yadda za su kusanceku su yi maku ɗa’a da biyayya. Ba lallai sai kun zauna kun wuni a gida ko kun ware masu rana ta musamman ba. Amma dai aƙalla a ce kun samu lokacin da za ku ci abinci tare, ko da ba a kwano ɗaya ba, ya zama dai a muhalli ɗaya.

Zama da su lokacin da ka ke cikin bacin rai, zai basu damar gane yadda ake haɗiye fushi da dauriya. Sannan fara’a da wasan zolaya yayin da ake cikin farin ciki zai ƙara masu sakewa cikin nishaɗi. Ko ba ka furta komai ba, kallo kawai ko murmushi, ko taɓawa ya wadatar da ya nuna irin abin da ke zuciyarka game da su.

Ina fatan hukumomin da abin ya shafa za su yi la’akari da abubuwan da ke faruwa a sassan ƙasar nan da suka shafi rashin tsaro, yunwa da talauci da yawaitar yara ’yan gudun Hijira a sansanoni, shigar yara ƙanana ƙungiyoyin asiri da ta’addanci da kuma ƙalubalen satar yara, ana yanyanka sassan jikin su da yi musu fyaɗe, domin ɗaukar matakan da suka dace na kyautata makomar yara da tsare martabar su.

A yayin da kotu a Jihar Kano ke gudanar shari’ar waɗanda ake zargi da yi wa Hanifa kisan gilla, muna roƙon ɓangaren shari’a da gwamnati su tabbatar da an yi adalci da kuma samar da tsauraran dokoki na kula da rayuwar ƙananan yara da kare haƙƙokin su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *