Ƙarancin fetur: Gunagunin ’yan Nijeriya ya sa NNPC kwana rabon mai

Daga AMINA YUSUF ALI

A ranar Talatar da ta gabata ne Kamfanin dillancin man Fetur a Nijeriya, NNPC, ya bayyana cewa, sashensu na rarraba man fetir ga ‘yan kasuwa masu sari ya fara kwana yana aiki domin tabbatar da an sallami dukkan motocin dakon man da suka zo ɗaukar man.

Daraktan Zartaswa na ɓangaren rarraba man na Kamfanin NNPC ɗin, Adetunji Adeyemi shi ya bayyana wa ‘yan jarida hakan a Abuja. Inda ya ƙara da cewa, a yanzu haka kusan lita biliyan biyu da kusan rabi na man fetur za a shigo da shi ƙasar nan kafin nan da ƙarshen wannan watan domin tabbatar da an samu wadatuwar man da za a rarraba shi ga ‘yan kasuwa, masu sayar da shi ga al’umma.

Waɗannan bayanai na Daraktan zartarwar sun zo ne  bayan kwana guda da aka samu tsananin ƙarancin man fetur ɗin a Birnin Tarayya, Abuja da Legas. Inda aka samu cincirindon motoci a gidajen mai suna dakon samun man.

Adeyemi ya bayyana cewa, an samar da wasu mutane da za su tabbatar da rarraba man a faɗin ƙasar nan ba tare da an samu tangarɗa ba. 

Ya ƙara da cewa, NNPC tana sane da ƙarancin man fetur ɗin da ya addabi mutane a kwanakin nan wanda ya faru ne sakamakon ɓullar wani gurvataccen mai wanda a yanzu hukumar ta killace shi ta hana sayar da shi. Don haka, ta ƙuduri aniyar shigo da litoci biliyan biyu da kusan rabi na man fetur daga waje, don a samu ya wadata a ƙasar nan, kafin nan da ƙarshen wannan watan na Fabrairun 2022.

Kuma ya ba da tabbacin cewa, dukkan man da ake sayarwa a gidan man ƙasar nan ingantattu ne. Kuma daga hukumar ta NNPC suke. Don haka, hukumar take buxiewa na tsahon awanni 24 kowacce rana domin tabbatar da kwalliya ta biya kuɗin sabulu. 

Gunaguni kan tashin gwauron zabin farashin fetur:
Tun daga ranar Talatar da ta gabata ne dai daɗaɗɗiyar matsalar ƙarancin mai fetur ta ƙara tsananta a ƙasar Nijeriya. Abinda ya tsananta wa ‘yan Nijeriya biyan Naira 600 zuwa Naira 700 a kan kowacce litar man fetur ɗin. 

Waɗanda da wahalar man ta fi tsanantawa a gare su su ne, mazauna Birnin Tarayyar Abuja da kuma jihar  Legas.

A makon da ya gabata ne dai hukumar da take kula da ingancin mai ta Nijeriya ta gano almundahana a cikin man fetur ɗin inda ta dakatar da cigaba da sayar da shi. Abinda ya jawo ƙarancin man.

Bayan afkuwar hakan ne, sai shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya ba da umarni ga hukumomin da suka dace don a hukunta dukkan waɗanda suke da hannu a cikin shigo da gurɓataccen fetur ɗin cikin Nijeriya.

Kodayake, an samu tabbaci daga hukumar NNPC a kan cewa za a shawo kan matsalar nan ba da daɗewa ba. Amma fa bisa dukkan alamu, matsalar da wuya a iya shawo kanta a kwana kusa. 

Rahotanni sun nuna cewa, hatta masu hawan abun hawa na gida da na haya sun ɗanɗana kuɗarsu. Inda aka samu suna kashe ninkin kuɗin da suke biya a baya idan za su je wani waje.

 A wani ɓangaren kuma, ‘yan kasuwar mai na ɓunɓurutu sun ci karensu babu ko babbaka. Inda su ma masu hayar ababen suka samu damar ƙallafa wa mutane ƙarin kuɗin abun hawa son ransu. 

Wata majiya ta bayyana cewa, a hanyar zuwa wani filin jirgi a Abuja ‘yan bunburutu sun jera hajarsu reras. A jikin kowacce jarkar man fetur mai lita 10 an liƙa farashinta Naira 7000 ko 6000. Sannan kuma su ma gidajen mai ba a bar su a baya ba. Domin su ma suna sayar da man a kan farashin Naira 190 zuwa Naira 195 kowacce lita.

Wani gidan mai da ya zanta da wakilin BLUEPRINT kuma ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa, suna sayar da abinda suka riga suka saya ne domin su samu riba. Kuma ba yadda suka iya. 

A yayin haɗa wannan rahoto dai, wakilin Blueprint ya ci karo da dogayen layuka na kusan kilomita 2 a gidajen mai a garin na Abuja. Inda wani matuƙin motar haya mai suna, Michael Conoil  ya bayyana masa cewa, ya wuni cur, a layin mai. 

A jihar Legas kuma, mutanen gari ne suke zargin direbobin haya da ƙarin kuɗin mota da gangan.  Inda wani mai suna, Oluwole Kadiri, ya shaida wa wakilinmu cewa, direbobin sukan yi amfani da irin wannan damar domin qarin kuɗin ababen hawa. 

Rahotanni sun bayyana cewa, a yankin Biktoriya na jihar kuwa, an ce har gidajen mai ma suna zaɓar wasu mutane waɗanda su kaɗai za su sayar wa da man.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *