Ƙarancin fetur ya jagwalgwala rayuwar ’yan Nijeriya

*Za a warware matsalar ba jimawa – Gwamnati

Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja

’Yan Nijeriya na cigaba da fuskantar azabar ƙarancin man fetur a ƙasar yayin da hukumomi suka ce su na yin aiki a wani yunƙuri na magance matsalar ƙarancin man da ya janyo raguwar kuɗaɗen shiga a kowane fanni.

Birnin Abuja da manyan jihohin Nijeriya sun afka cikin matsanacin ƙarancin man fetur duk da alƙawarin da mahukunta suka yi na samar da shi. Wannan ya kawo cikas a harkokin yau da kullum, saboda ana sayar da shi da tsada, sannan kuma ga wuyar samu.

A lokuta da dama, gardama kan ɓarke a tsakanin dubban masu motoci da babura mai ƙafa uku da suke rige-rigen shiga gidajen mai a Abuja, Babban Birnin Tarayyar Nijeriya, da ma wasu jihojin ƙasar, saboda mummunan ƙarancin man fetur da ake fuskanta.

Wannan matsalar ta durƙusar da al’amura a sassa daban-daban na Abuja da ma wasu jihohi da dama na qasar. Sannan lamrin ya buɗe kasuwar bayan fage ta ’yan bumburutu, inda kowace litar man fetur ta kan kai Naira 700 zuwa 800 maimakon Naira 165 a farashin gwamnati, duk da cewa dai, a yammaci zuwa daren jiya an fara ganin alamun farashin yana sauka.

An shafe kusan mako guda kenan ana fama da matsananciyar wahalar man fetur a Nijeriya, kama daga bazuwar wani gurɓataccen man da ya riƙa lalata ababen hawan mutane aka fara samun dogwayen layuka a gidajen mai da kuma sayen man da matuƙar tsada.

Hukumomi dai tuni suka yi bayanin dalilan da suka sa aka samu yaɗuwar gurɓataccen man, wanda zuwa yanzu an dakatar da sayar da shi.

Amma har yanzu ba su bayar da wani bayani mai gamsarwa na dalilin da ya sa man ya ke wahala ba. Sai dai kamfanin mai na Nijeriya NNPC ya ce, wannan rashin man da ake fama da shi a yanzu ya samu ne, saboda killace miliyoyin litocin gurɓataccen man da ya bazu a kasuwa. Sai dai ’yan Nijeriya da dama na neman gani a ƙasa akan iƙirari na wadata ƙasar da man fetur.

Nijeriya dai ta dogara ne akan shigo da man fetur, saboda gaza gyara matatun man fetur ko kuma gina qari kan waɗanda ake da su, kuma har yanzu ba labarin gina wasu sabbi duk da yanayin arzikin da Allah ya hore wa qasar, amma ana yanayi na ga ƙoshi ga kwanar ’yunwa.

Matsalar ƙarancin man ya jawo wa ’yan Nijeriya matsaloli da dama, kamar toshe hanyoyi, ƙarin kuɗin abin hawa da tsadar wasu abubuwa, yini ka kwana a layi, dambe da zage-zage a layin mai da dai sauransu.

Ita ma Ƙungiyar Ƙwadago ta Nijeriya (NLC), ta yi Allah-wadai da matsalar ƙarancin man fetur da ake fama da shi a faɗin ƙasar, lamarin da ya jefa miliyoyin ’yan Nijeriya cikin mawuyacin hali, inda ta ce ta ɗauki matsayi.

Shugaban NLC, Ayuba Wabba ne ya bayyana hakan a ranar Laraba a Abuja, a wata sanarwa mai taken ‘Matsayin Ma’aikatan Nijeriya akan Taɓarɓarewar Muhimmancin Ƙasa’.

Wabba ya ce, ƙungiyar ta NLC ta lura da sake ɓullowar al’amura da dama da ke da matuƙar muhimmanci a ƙasa.

Amma Kamfanin Man Fetur na Nijeriya (NNPC) ya ce, ya fara aikin tuƙuru kuma cikin sa’o’i 24 za a warware matsalar ƙarancin man fetur. Kamfanin NNPC ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata a Legas.

Ita kuma Hukumar Kula da Raba Man Fetur ta Nijeriya (NMDPRA) ta bayar da umarnin a ƙara tsaurara matakan tsaro a gidajen mai, domin duba ayyukan ɓarayi da dillalan kasuwar bayan fage.

Ogbugo Ukoha, Babban Daraktan Hukumar NMDPRA, ne ya bayar da wannan umarni ne a yayin wata ziyara da ya kai wasu gidajen mai a Apapa da ke Jihar Legas ranar Alhamis.

Ya kuma nemi afuwar ’yan Nijeriya kan matsalolin da ake fama da su a halin yanzu na ƙarancin man fetur, yana mai cewa abin takaici ne matuƙa.

Idan dai za a iya tunawa, a shekarun baya ƙarancin man fetur a Nijeriya ya fi zama ruwan dare, amma bayan zuwan Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari a shekara ta 2015 lamarin ya nemi ya zama tarihi, musamman bayan wahalar man da aka sha a ƙarshen shekara ta 2015 ɗin. To, amma ’yan Nijeriya sun cigaba da ƙorafin tsadar farashin man, wanda gwamnatin ta gada akan Naira 87, ita kuma ta mayar da shi Naira 165 sakamakon fara janye tallafin mai da ta yi, wanda har yanzu ake yin kiki-kaka kan cire ɗumgurungum.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *