Ƙungiyar matasa masu yaƙi da miyagun ƙwayoyi sun karrama Inuwa Waya

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

Ƙungiyar matasa masu yaƙi da miyagun kwayoyi ta ƙasa haɗin gwiwa da ofishin mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Obi Omo Agege, sun karrama Malam Inuwa Waya bisa ƙoƙarin da yake wajen yaƙi da sha da fataucin ƙwayoyi.

Da yake bayani bayan karramawar, Malam Inuwa Ibrahim Waya wanda jigo ne a jam’iyyar APC kuma yake neman tsayawa takarar Gwannan Kano a zave na gaba, ya ce, Gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin Gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje ta sa ilimi kyauta kuma dole, saboda haka sai an taimaka ma ta a wannan fannin, shi ya sa shima yake irin wannan taimako ta raba littattafai, kayan rubutu, jakankuna da kayan makaranta na maza da mata a makarantun boko da na Islamiyya.

Ya ce, duk wani waje da ya je zai yi jawabi, yana yawan faɗakarwa ta jawo hankalin yara su gujewa shaye-shaye da kuma aikata miyagun ɗabi’u.

Inuwa Waya ya ce, kullum yana jan hankalin matasa da cewa duk wani ɗan siyasa da suke bi ya ce su shiga su yi daba ko jagaliyanci su ce masa ya kawo ɗansa ko ’yarsa su shiga musu gaba kafin su tafi.

Ya qara da cewa, irin wannan shi ya sa yake ganin wannan qungiya ta matasa da haɗin kan ofishin mataimakin Shugaban majalisar Dattawa suka kirawoshi suka  ba shi wannan kyauta don zaburantar da shi a kan cigaba da ƙara ƙaimi da kwazo a kan abubuwa da yake aiwatarwa.

Inuwa Waya ya ce, wannan karramawa da aka yi masa abin farin cikine ga ’yan siyasa masu son zaman lafiya irinsa kuma zai cigaba da gudanar da abin da yakamata wajen taimakawa a kauda ɗabi’ar shaye-shaye a tsakanin matasa don su zama nagartattu masu amfanar da al’umma.