Ƙungiyar GCAF ta samu nasarorin tallafa wa mabuƙata da dama, inji Ambasada Ɗanlarabawa

Ambasada Ɗanlarabawa


Gidauniyar Tallafa wa mabuƙata daga tushe (wato Grassroot Care and Aid Faudation) gidauniya ce da ta dukufa wajen ayyukan jinƙai musamman a Arewacin ƙasar nan, a wannan tattaunawa da muka yi da shugabanta Ambasada Auwal Muhammad Ɗanlarabawa za ku ji irin faɗi tashin da wannan Gidauniya ta yi cikin shekaru 10 da kafuwarta ku biyo mu donmin jin yadda tattauawar mu za ta kasance:

Daga IBRAHIM HAMISU KANO

Masu karatun mu za su so sanin cikakken sunan ka da taƙaitacen tarihin ka?
Suna na Ambasada Auwal Muhammad Ɗanlarabawa an haife ni a Gama dake Ƙaramar Hukumar Nassarawa a Jihar Kano, anan na yi karatu sannan kuma na yi tafiye tafiye da hada-hada da dama na harkokin gwagwarmaya a kan ceton rayuwar al’umma.

Ka kasance Shugaba kuma mu’assasin ƙungiyar Grassroot Care and Aid Faudation (GCAF) ta yaya ƙungiyar ta samo asali?
Na ƙirƙiri wannan gidauniya ne a bayan dawowa ta Nijeriya, bayan na yi wasu ayyukan ceto na agaji  a wasu ƙasashe guda biyar, wanda wannan yasa na ƙirƙiri wannan gidauniya dan a taimaka wa rayuwar marayu da mabuƙata, kuma na raɗa mata suna Foundation for the Support of Less Privileged daga baya ta koma Grassroot Care and Aid Foundation wato  sabida neman sahalewar hukuma ta CAC da yi mata dukkan wasu abubuwa da ake wa gidauniya a hukumance.

Mene ne maƙasudin kafawa da manufofin wannan ƙungiya?
Maƙasudin kafa ta shi ne a samar da wata dama ga mutane da suke cikin wani hali za su dinga samun kulawa ta hanyar bibiya lungu da saƙo, ana duba rayuwar su ana kuma tallafa musu. Musanman marayu da mabuƙata waɗanda basa bara sannan suna iya ƙoƙarin ganin sun yi rayuwa ta dogaro da kai, Manufar kafa ta shi ne ta zama gidauniya da take bai wa masu son taimaka wa mabuƙata amma basa samun wanda za su bai wa kuma yaje inda ake buƙata. Ma’ana mu muka fara bada damar mutane su zo mu samar musu da mabuƙata da suke nema su taimaka musu, mu zama masu sada mabuƙata da mawadata, buɗe hanyar da za a taimaka wa al’umma da ya kamata, a ɓangaren lafiya, ciyarwa, agajin gaggawa, faɗakarwa, koyar da sana’a, tallafa wa marayu a ɓangaren ilmi, samar da ruwan sha, gina masallatai, asibiti, burtsatse, da sauran su.

A Jihar Kano gidauniyar take ayyukan ta ko ta tsallaka wasu jihohin?
Gidauniyar ayyukan ta ba iya Kano ya tsaya ba, sannan muna da mutanen mu da muke aiki da su a sauran wasu jihohi na ƙasar nan, sai dai babban offishin ta yana nan jihar Kano in da aka ƙirƙiro ta.

Yaushe aka kafa ƙungiyar ?
An kafa wannan gidauniya ne a ranar 1-1-2011 wanda kuma tun daga wannan rana gidauniyar ta fara ayyukan ta gadan gadan har zuwa wannan lokaci ba tare da gajiyawa ba, kuma alhamdu lillah gidauniya na ta cigaba.

Ta ina kuke samun kuɗin shiga da kuke tafiyar da wannan ƙungiya?
Hanyoyin samun kuɗin wannan gidauniya kala kala ne, na farko dai shi ne ta hanyar tattara kuɗin wata wata da ‘yan gidauniya ke bayarwa, sannan akwai bayin Allah da idan muka sanar da za mu yi wani abu suna shigowa a yi aikin da su, sannan akwai tsarin nan na watsa bayanai a kafafen sada zumunta inda duk mai son shiga tsarin zai bada gudunmawa, wannan shi ne tsarin da muke da shi na hada-hadar samar da tsarin kuɗin shiga a wannan gidauniya.

Duba da halin da arewa ke ciki na halin rashin tsaro akwai ‘yan gudun hijira da mata da yara da aka mutu aka bari mai kungiyarku take akai?
Muna daga cikin masu tallafawa ‘Yan gudun hijra da kayan sawa, kayan abinci, da koyar da sana’a mun daɗe a wannan tsari, sannan suna daga cikin waɗanda suke karatu a makarantun mu na marayu da muke dasu Wanda aka saka wa suna Grassroot Community School kuma muna da su a wurare daban daban, sannan mukan ba su jari yadda za su dinga yin wani abu suna samun abinda za su biya wasu buƙatun nasu maimakon su je suna yin barace-barace.

Ta ina wannan ƙungiyar ta ku ta sha banban da sauran ƙungiyoyin jin ƙai na Arewa duba da yadda za ka ga wasu na yin awon gaba da tallafin da akan ba su?
Muna da tsari wanda ya sha banban da sauran ƙungiyoyi a wajen aiki. Farko muna bada dama ga mai bayarwa yazo ya bayar da kan shi ko da kan ta, na biyu muna son a aiko wakili ga wanda ba su da lokaci, na uku muna ɗaukar komai da muka gudanar mu aika wa wanda ya ba mu gudunmawa yayin karɓa da lokacin rabawa da kuma bayanai na waɗanda aka bai wa ko da za a bibiya daga baya, sannan muna ƙoƙarin ganin dukkan waɗannan abubuwa an yi su a kowanne lokaci. Dan hakan ma a wannan gidauniya ta mu kofa a buɗe take na ba wa masu ba mu gudunmawa su bibiyi abin da suka ba mu a kowanne lokaci. Bin wannan ya sa yanzu mun kai wani mataki na zama masu sanya idanu akan ayyukan da aka bai wa wasu dan a tabbatar da sun yi abin da ya dace in sun je neman taimako ko idan an ba su abin da za su rabar. Ko a aiko mana ace muje mu tabbatar idan gaskiya ne mu ba su ko mu sa a ba su.

Daga lokacin da aka kafa wannan ƙungiyar zuwa yanzu waɗanne nasarori za ka iya cewa an samu?
Mun samu nasarori da dama har ma wasu ba za su iya faɗuwa ba saboda yawan su, farko mun samu damar raba jari ga mabuƙata gida gida na mutane 2000 a shekarar 2013, mun yi aƙalla burtsatse 60 a wurare daban daban zuwa yanzu, muna da marayu 1500 da suke ƙarƙashin wannan gidauniya ana kula da karatun su a makarantun mu na marayu da muke da su namu na kan mu waɗanda ake karatu kyauta, mun biya wa marasa lafiya da dama kuɗin aiki a asibiti, raban kayan agaji na abinci wannan gidauniya ita ta fara bada kayan agaji na korona a faɗin ƙasar nan, ciyar wa ta azumi na tsawo shekaru 9, shirya bitoci kala kala a kan zamantakewar rayuwa, koyar da sana’a ga ‘yanmata, zawarawa, da ba wa masu ƙaramin ƙarfi jari haɓaka sana’o’in su. Bayar da bashi mara ruwa, gina masallatai da gyarawa har 62, runfunan makarantun 22, raba littattafai ga ɗalibai a makarantun islamiyya da boko, da sauran wasu abubuwan da dama.

Ƙalubale fa akwai ko babu?
Kalubalen su ma suna da yawa sosai, mutane na ba mu matsala wajen rashin fahimtar ayyukan mu, wanda kowanne idan yana da matsala wajen mu zai zo idan ba a masa ba yace zaɓe ake, Wanda ba mabuƙata ba ne amma sai su dage da sai an basu abinda aka tanada dan mabuƙata ko marayu, rashin shigowar gwamnati cikin ayyukan mu, ‘yan damfara da ke ƙoƙarin sai sun cutar, rashin tallafawa ayyukan ita kanta gidauniyar wajen kayan aiki. Waɗannan suna cikin ƙalubalen da muke fuskanta.

Ta ina kake ganin irin waɗannan ƙungiyoyin naku za su taimaka wajen kawo ƙarshen rashin tsaro a yankin mu na Arewa?
Rashin tsaro wani Abu ne da yake da sarƙaƙiya sosai, kuma yake da hatsari duba ga halin da tsaro yake ciki a wannan yankin namu. Amma idan da za a taimaka wa al’umma yadda ya kamata wajen yaƙi da talauci, ɗaukaka rayuwa, samar da aikin yi da farfaɗo da kamfanoni da tabbatar da agaji na zuwa wajen dukkan mabuƙata ba tare da an tare su a hanya ko an karkatar dasu ba, ɗaukar mataki akan rahoton abubuwa akan lokaci,  wannan zai taimaka.  Ƙarshe kuma a saka rayuwar al’umma ita ce a kan gaba ba kuɗi ba, sannan a samar da haɗin kai daga shugabanni da mabiya, a samar da soyayya ta gaskiya.

Mene ne fatanka na ƙarshe?
Fatana shi ne al’umma su canja daga halayen da suke da shi na rashin shigowar su cikin ayyukan ceto, dan inganta rayuwar al’umma, kama daga gwamnati da sauran masu ƙarfi, sannan su duba gidauniyoyin da suke aiki na gaskiya su ja su a jiki, su yi aiki da su, kuma Ina fatan duk wanda ya karanta wannan hira da ya shigo mu yi wannan tafiya da shi ko da it,a wajen tallafa wa wannan gidauniya musamman a ɓangaren gina gobe kiyama na ayyukan sadaƙa mai gudana, musamman waɗanda mu ke yi na makarantun marayu da kuma sauran ayyukan mu dan su yi wa kan su ko iyayen su waƙafi da za su ke samun lada mai gudana a gobe ƙiyama. Sannan kuma godiya da irin gudunmawa da wannan kamfani na jarida ke bayarwa ga irin wannan gidauniya Allah ya saka muku da alkhairi ya ƙara ɗaukaka Manhaja.

Madallah! mun gode.

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*