Ɗan Bafarawa, mai neman kujerar Gwamnan Sakkwato a PDP, ya tsallake rijiya da baya

Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato

Mai son tsayawa takarar gwamnan Sakkwato a tutar jam’iyyar PDP a zaɓen 2023 kana ɗa ga tsohon gwamnan jihar Sakkwato, Sagir Attahiru Bafarawa ya tsallake rijiya da baya ne bisa ƙoƙarin hallaka shi da wasu da ake zargi ɓatagari ne da yunƙurin yi a Sakkwato.

A wani bayani da dandalin goyon bayan Sagir Bafarawa suka fitar, sun bayyana cewa wani sanannen ɓatagari a Sakkwato Alu KC ne suka dirar wa gidan Sagir da nufin hallaka shi jim kaɗan bayan kammala sallar Taraweeh a daren ranar Talata wanda ya tsallake rijiya da baya a lokacin.

“Yau Talata 19 ga watan Afrilu, 2022, wani Alu KC ya yi yunƙurin hallaka Sagir Bafarawa a gidan sa bayan kammala sallar Taraweeh, sai dai yunƙurin nasa bai zo da nasara ba,” cewar bayanin.

Lamarin da ya sanya ƙungiyar yin mamaki da faruwar lamarin, dama barin ɓatagari na cin karen su babu babbaka cewar ƙungiyar.

Duk yunƙurin da wakilin mu ya yi na jin ta bakin Sagir ɗin ya ci tura domin wayar sa a kashe, sai dai wata majiya ta kusa ga ɗan takarar gwamnan tuni ta tabbatar da faruwar lamarin.

Sagir Bafarawa dai shine mutum na farko da ya soma nunar sha’awar sa ta tsayawa takarar gwamnan Sakkwato a PDP a zaɓen 2023 mai ƙaratowa.