Ɗan jarida, Jibrin Ndace ya wallafa littafi uku kan matsalar tsaron Nijeriya

Daga AISHA ASAS

Fitaccen ɗan jaridar nan kuma mai sharhi akan al’amuran jama’a, sannan kuma wanda ya samu lambar yabo da dama a Nijeriya, Jibrin Baba-Ndace, na shirin ƙaddamar da littafai uku, wanda zai bayyana ‘Yaƙin Sojojin Nijeriya da ‘yan ta’addan Boko Haram da ISWAP a Arewa maso Gabas.

Littattafan suna ɗauke da taken: Walking the War Front with Lt. Gen. TY Buratai,” “Duty Call Under Buratai’s Command” da kuma “The Lonely Grave and Other Poems__ an anthology.’

A wata sanarwa da Mista Ndace ya fitar, ya ce za a gudanar da taron bajekolin littafan ne a babban birnin tarayya Abuja, nan ba da jimawa ba.

Ya bayyana littafinsa na uku a matsayin abin da ya zama wajibi a karanta shi ga duk wanda ke neman samun zurfin fahimta da kuma shaida na hoto kan yaƙin da ake yi da ‘yan tada ƙayar baya a Nijeriya a mafi munin lokaci.

Da yake ƙarin haske kan dalilin da ya sa ya fara aikin wanda ya ɗauki tsawon shekaru biyar yana yi ba dare ba rana, Ndace, tsohon babban sakataren yaɗa labarai ga Gwamna Abubakar Sani Bello na Jihar Neja, ya ce ya samu ƙwarin guiwa da buƙatar samar da ƙwarewa akan yaƙi da tada ƙayar baya a Nijeriya.

“Waɗannan litattafan sun samu ƙwarin gwiwa daga tsoffin sojoji da suka yi yaƙi a ciki da wajen yaƙin.

“Sojojin da suka sadaukar da rayuwarsu don yi wa babbar al’ummarmu hidima, jajircewar da suka nuna da kuma abubuwan da suka faru na ban tsoro.

“Daga cikin sojoji da masu yi wa ƙasa hidima, Laftanar Janar TY Buratai ya mamaye babban vangare na labarin.

“Lt. Janar TY Buratai tsohon Hafsan Sojin Nijeriya ne mai ritaya, wanda aka naɗa a shekarar 2015 kuma ya yi ritaya a watan Janairun 2021,” inji shi.

Dangane da batun littafin, wakilin jami’in tsaro na Ace, ya bayyana cewa ƙoƙarin nasa zai kasance wani abin da ba a zata ba ne da aka bayyana ta hanyar bayani na farko, waƙoƙi, hotuna, da bada labari mai ƙarfi, wanda ya shaida irin jajircewa da sadaukarwar da sojoji suka yi, da mugunyar haqiqanin faɗace-faɗace da kuma irin nau’in da yaƙi ke yi wa jikin mutum da kuma tunanin mutum.

Wani jami’in soja da ya ga rubutun littattafan, ya bayyana cewa: “Waɗannan littafan da aka kwashe sama da shekaru 5 don ganin an samu nasarar kammalawa, Jibrin ya sha gumi da zubar hawaye wajen ganin sun kammalu.

“Waɗannan littattafan ba labari ba ne kawai sai zahirin gaskiya ba kawai ta idanunsa ba, har ma ta hanyar abubuwan da wasu ma’aikatan suka yi.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *